An Kama Ma'aikacin Gwamnatin na Satar Takalmi a Masallacin wajen Aikinsu
- Gwamnatin Jihar Bauchi ta dauki mataki kan wani jami’in kashe gobara da aka samu da laifin satar takalman jama’a a lokacin ibada
- Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi ta dakatar da aikin Abdulkadir B. Aliyu, wani Babban Sufeto na Kashe Gobara
- Rahoto ya nuna cewa an dauki matakin ne bayan kammala dukkan matakan ladabtarwa da dokokin aikin gwamnati suka tanada
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Bauchi – Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi ta kori Abdulkadir B. Aliyu, wani Babban Sufeto na Hukumar Kashe Gobara ta jihar, bisa zargin aikata laifin sata da sauran munanan dabi’u.
Aliyu, wanda ke aiki a sashen Hukumar Kashe Gobara na Ma’aikatar Ayyuka da Sufuri, an same shi da laifin satar takalman jama’a a lokacin da suke gudanar da sallah a Babban Masallacin Sakatariyar Abubakar Umar da ke Bauchi.

Source: Twitter
An kori jami'in gwamnati a Bauchi
Rahoton Leadership ya nuna cewa an dauki matakin ne yayin zaman taro na 32 na Hukumar Kula da Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Bauchi.
Bayanan da Legit ta samu sun nuna cewa jami’in yada labarai na hukumar, Saleh Umar, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.
Hukumar ta ce ta bi dukkan matakan ladabtarwa da dokokin Aikin Gwamnatin Jihar Bauchi suka tanada kafin daukar matakin korar Aliyu.
Laifin da aka same shi da shi
Sanarwar ta ce abin da Aliyu ya aikata ya saba wa ka’idojin aiki na 0312 (ix da xii) na dokokin aikin gwamnati da suka shafi rashin da’a.
Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta kuma bayyana cewa ba wannan ne karon farko da aka taba daukar mataki kan jami’in gwamnatin ba.
A ranar 29 ga Satumba, 2025, an taba ba Aliyu gargadi mai tsanani saboda barin wurin aikinsa ba tare da izini ba.
Haka kuma an tuhume shi da sakaci wajen gudanar da aiki karkashin sashe na 0312, abu na 4 na dokokin aikin gwamnati na jihar.

Source: Original
An gargadi ma’aikatan gwamnati
A yayin zaman, mambobin hukumar sun yaba wa Sakataren dindindin kuma magatakardar hukumar, Alhaji Yakubu Bello, kan jajircewarsa wajen gudanar da ayyukansa.
Sun yaba da kokarinsa wajen tafiyar da harkokin gudanarwa da kuma bayar da gudunmawa wajen inganta ayyukan hukumar.
Shugaban hukumar, Dr Ibrahim Alhaji Muhammad, ya sake jaddada kudirinsa na kare mutuncin hukumar ta hanyar tabbatar da bin dokoki da ka’idojin aiki.
Ya kuma gargadi ma’aikatan gwamnati a jihar da su guji aikata duk wani nau’in rashin da’a yayin gudanar da ayyukansu.
Isa Yuguda na raye
A wani labarin, mun ruwaito cewa wani makusancin tsohon Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda, ya musanta rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta cewa tsohon gwamnan ya rasu.
Makusancin tsohon gwamnan, Alhaji Salisu Barau, ya bayyana rahoton a matsayin karya marar tushe, yana mai cewa Yuguda yana raye kuma yana cikin koshin lafiya.
Wani makusancin tsohon gwamnan kuma tsohon hadiminsa, Hon. Abdulmumini Kundak, shi ma ya musanta rahoton tare da bayyana shi a matsayin labarin karya.
Asali: Legit.ng

