Kungiyar Musulmai Ta Gano Wuri 1 da Shettima Ya Yi Kuskure a Taron Majalisar Dinkin Duniya

Kungiyar Musulmai Ta Gano Wuri 1 da Shettima Ya Yi Kuskure a Taron Majalisar Dinkin Duniya

  • Kungiyar musulmi ta MPAC ta soki Gwamnatin Tarayya kan rashin ambaton Falasɗinu a jawabin Najeriya a taron UNGA 81
  • Kungiyar ta ce Najeriya ta ambaci Gaza da Falasɗinu a taron Majalisar dinkin duniya na bara, amma ta yi shiru a jawabin 2026
  • MPAC ta bukaci Najeriya ta ƙara bayyana matsayinta kan rikicin Isra’ila da Falasɗinu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Kungiyar Harkokin Musulmi (MPAC) ta Najeriya ta soki Gwamnatin Tarayya kan rashin ambaton Falasɗinu a jawabin Najeriya a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81 (UNGA 81).

Kungiyar ta ce Najeriya ta yi tsokaci sosai kan halin da ake ciki a Gaza yayin babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na baya, amma ba ta ambaci Falasɗinu, ko tsarin ƙasashe biyu ba a cikin jawabin da ta gabatar a 2026.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 7 da Najeriya ta nema a taron UNGA karo na 81

Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima yana jawabi a babban taron Majalisar dinkin duniya karo na 81 a birnin New York na kasar Amurka Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Daily Trust ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar, Disu Kamor, ya fitar ranar Juma’a.

MPAC ta ce jawabin Najeriya na baya-bayan nan ya ƙunshi batutuwa da suka haɗa da gyaran Majalisar Tsaro ta Majalisar Ɗinkin Duniya, kuɗaɗen yaƙi da sauyin yanayi, tsarin basussukan duniya da yaƙi da ta’addanci a yankin Sahel.

Sai dai kungiyar ta ce jawabinmai sakin layi 24, wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya gabatar, bai ambaci Falasɗinu ko sau ɗaya ba.

MPAC ta kwatanta jawaban Najeriya

A cewar kungiyar, wannan matsayi na Najeriya ya bambanta da jawabin da ta gabatar a taron UNGA 80, inda ta yi Allah-wadai da kisan fararen hula a Gaza tare da sake jaddada goyon bayanta ga tsarin ƙasashe biyu.

“Ba a ambaci Gaza ba. Ba a ambaci al’ummar Falasɗinu ba. Tsarin ƙasashe biyu — kalmar da Najeriya ta yi amfani da ita ‘ba tare da jinkiri ko shakka ba’ watanni 12 da suka gabata — ba a ambace ta ko sau ɗaya ba,” in ji MPAC.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Shettima ya fada kan Najeriya a taron majalisar dinkin duniya

Kungiyar ta danganta wannan sauyi da abin da ta bayyana a matsayin ƙara kusantar dangantakar tsaro da diflomasiyya tsakanin Najeriya da Isra’ila tun bayan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta hau mulki a watan Mayun 2023.

Ta kawo misalin yarjejeniyar haɗin gwiwar tsaro da Najeriya da Isra’ila suka sanya hannu a watan Agustan 2025, da kuma rahotannin hulɗa kan musayar bayanan sirri, fasahar sa ido da horas da jami’an yaƙi da ta’addanci.

MPAC ta kuma ambaci shirye-shiryen kafa Kwamitin Haɗin Gwiwa tsakanin Najeriya da Isra’ila da zai shafi tsaro, lafiya, fasaha da haɗin gwiwar tattalin arziki.

MPAC ta jero abin da take bukata

Kungiyar ta tambayi ko rashin ambaton Falasɗinu a sabon jawabin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya yana da alaƙa da ƙara zurfafa dangantakar ƙasar da Isra’ila.

MPAC ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta shiga ƙarar da Afirka ta Kudu ta shigar kan Isra’ila a gaban Kotun Ƙasa da Ƙasa (ICJ) kan zargin kisan kiyashi.

Kashim Shettima
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a taron Majalisar dinkin duniya Hoto: Kashim Shettima
Source: Facebook

Ta kuma ce ya kamata Najeriya ta sanya haɗin gwiwar tsaro da Isra’ila ya kasance ƙarƙashin sharadin yin hisabi kan ayyukan da ake zargin an aikata.

Kungiyar ta ƙara buƙatar Najeriya ta fito fili ta nuna goyon bayanta ga Falasɗinawa tare da ɗaukar matsaya mai ƙarfi kan rikicin.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta sauya dabara, ta cafke kasurgumin jagoran 'yan ta'adda

Abubuwan da Najeriya ta gabatar a UNGA

Kun ji cewa Najeriya ta nemi a bai wa Afirka kujerun dindindin biyu a Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya tare da cikakken iko da suka haɗa da hawa kujerar naki.

Najeriya ta yi kira da a fifita diflomasiyya, dokokin ƙasa da ƙasa, kare fararen hula da samar da tallafin kuɗi mai sauƙi ga ƙasashe masu tasowa

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262