Yan Bindiga Sun Rutsa Mutane a Zungureren Rami, An Rasa Rayuka da Dama
- Akalla masu haƙar ma’adinai biyar sun mutu yayin da wasu ’yan bindiga suka fitsa su a ramin hakar ma'adanai a jihar Filato
- Rahotanni sun nuna cewa wasu mutum biyu sun samu raunuka a harin da aka kai yankin karamar hukumar Barkin Ladi
- Mai magana da yawun kungiyar ci gaban kabilar (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Plateau, Nigeria - Akalla masu haƙar ma’adinai biyar aka harbe har lahira, yayin da wasu mutum biyu suka samu raunuka bayan ’yan bindiga sun kai hari a jihar Filato.
An ruwaito cewa maharan sun rutsa mutanen ne a wurin haƙar ma’adinai da ke ƙauyen Marit, ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta Jihar Filato, ranar Asabar.

Source: Getty Images
'Yan bindiga sun kashe mutum 5
Daily Trust ta rahoto cewa mai magana da yawun kungiyar matasan Berom (BYM), Rwang Tengwong, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce harin ya faru da misalin ƙarfe 1:00 na rana.
Ya ce:
“An kashe mutum biyar yayin da wasu mutum biyu suka samu raunuka a harin. Wannan lamari ne mai matuƙar ban tausayi da raɗaɗi.
“Muna Allah-wadai da wannan hari tare da kira ga hukumomin tsaro da su ɗauki matakan gaggawa domin kare al’ummominmu da kuma hana sake kai hare-hare.”
Mazauna yankin sun shiga jimami
Wani mazaunin yankin, Simon Mundat, shi ma ya tabbatar da faruwar harin, inda ya ce asarar rayukan ta yi matuƙar tayar da hankali.
Mundat ya ce:
“Muna matuƙar baƙin cikin wannan hari. An kashe mutum biyar, yayin da wasu biyu suka samu raunuka.
“Wannan lamari ne mai matuƙar raɗaɗi ga al’umma. Muna roƙon hukumomi da su ƙara tsaurara matakan tsaro a yankin domin mutanenmu su gudanar da ayyukansu na halal ba tare da tsoro ba.”
Ya zuwa lokacin da ake haɗa wannan rahoto, kakakin Operation Enduring Peace, Captain Polycarp Oteh, da na Rundunar ’Yan Sandan Filafo, SP Alabo Alfred, ba su ce komai ba kan harin.

Kara karanta wannan
Iska mai ƙarfi ta haddasa hatsarin jirgi, mata da dama sun rasa rayukansu a Najeriya

Source: Facebook
An ƙaƙaba dokar hana fita
Tun farko, gwamnatin jihar ta kakaba dokar hana fita daga magariba zuwa wayewar gari a ƙananan hukumomi uku, ciki har da Barkin Ladi, ranar Litinin domin dawo da doka da oda bayan hare-hare da kashe-kashe.
A cikin wata sanarwa da kwamishiniyar Yaɗa Labarai da Sadarwa ta jihar, Joyce Ramnap, ta fitar ranar Juma’a, gwamnatin ta yi Allah-wadai da hare-haren da ake ci gaba da kai wa mutanen yankunan.
Ta kuma yi kira ga mazauna yankunan da su kwantar da hankalinsu tare da bin doka da oda, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Rami ya rufta kan masu hakar ma'adanai
Kun ji cewa mutane huɗu sun mutu bayan wani ramin hakar ma'adanai ya rufta a yankin Baban Rafi da ke ƙaramar hukumar Bokkos ta Jihar Plateau.
Shugaban matasan Bokkos ya ce waɗanda abin ya rutsa da su sun haɗa da maza biyu da mata biyu, kuma danginsu sun karbi gawarwakinsu sun birne su.
Asali: Legit.ng
