MURIC Ta Gano Wurare 2 da Najeriya Ta Yi 'Abin Kunya' a Taron Majalisar Dinkin Duniya
- MURIC ta soki Najeriya kan zargin rashin saka batun Falasɗinu cikin takardar matsayinta a babban taron Majalisar dinkin duniya na 2026
- Kungiyar ta ce wakilan Najeriya sun ƙi shiga jerin ƙasashe 77 da suka fice yayin jawabin Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu
- MURIC ta buƙaci ’yan Najeriya da ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam su nemi gwamnati ta yi bayani kan matsayinta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Ƙungiyar Kare Haƙƙin Musulmi (MURIC) ta yi Allah-wadai da zargin cewa Najeriya ta kasa saka batun Falasɗinu cikin takardar matsayarta a babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya na 2026 (UNGA).
Haka zalika, MURIC ta caccaki matakin wakilan Najeriya ƙin shiga jerin ƙasashen da suka ficedaga zauren taron yayin jawabin Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu.

Source: Twitter
Leadership ta ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar kare hakkin musulmin ta fitar ranar Asabar, 26 ga watan Satumba, 2026.

Kara karanta wannan
Kungiyar musulmai ta gano wuri 1 da Shettima ya yi kuskure a taron Majalisar ɗinkin duniya
Abubuwa 2 da MURIC ta yi Allag wadai
Shugaba kuma wanda ya kafa MURIC, Farfesa Ishaq Akintola, ya bayyana matsayin Najeriya a taron na ƙasa da ƙasa a matsayin abin “mamaki, abin takaici, abin zargi da kuma abin ƙyama”.
Kungiyar ta yi zargin cewa Najeriya ba ta saka batun Falasɗinu cikin takardar matsayinta da ta gabatar a Majalisar Ɗinkin Duniya ranar Alhamis, 24 ga Satumba, 2026.
Ta kuma ce wakilan Najeriya sun ƙi shiga cikin ƙasashe 77 da suka fice daga zauren yayin da Netanyahu ke gabatar da jawabinsa.
MURIC ta Nuna damuwa
MURIC ta ce wannan matsayi da take zargin Najeriya ta ɗauka ya fi tayar da hankali saboda girman matsalar jin ƙai da ake fuskanta a Gaza.
Kungiyar ta ambaci alkaluman da ta ce sun nuna cewa an kashe Falasɗinawa fiye da 73,922, yayin da kimanin 174,995 suka samu raunuka, sannan cibiyoyin kiwon lafiya a Gaza suka kai matukar tabarbarewa.
Ta kuma yi zargin cewa an lalata manyan sassan Gaza, yayin da mata da yara suka kasance cikin adadi mai yawa na waɗanda aka kashe da waɗanda suka samu raunuka.
A cewar MURIC, Falasɗinawa na kuma fuskantar ƙarancin abinci, ruwa, man fetur da wutar lantarki, yayin da yara da mata masu juna biyu ke daga cikin waɗanda lamarin ya shafa.

Source: Facebook
Ta nemi gwamnatin Najeriya ta yi bayani
MURIC ta yi kira ga ’yan Najeriya masu imani da adalci da daidaito da su nemi Gwamnatin Najeriya ta yi wa jama’a bayani tare da ɗaukar alhakin matsayinta kan batun Falasɗinu.
Ta kuma buƙaci ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam a Najeriya su fito su yi magana kan abin da ta kira “matsayar da abin takaici” da ƙasar ta ɗauka game da batun Falasɗinu.
MPAC ta soki jawabin Najeriya a UNGA
Kun ji cewa kungiyar musulmi ta MPAC ta soki Gwamnatin Tarayya kan rashin ambaton Falasɗinu a jawabin Najeriya a taron UNGA 81.
Kungiyar ta tambayi ko rashin ambaton Falasɗinu a sabon jawabin Najeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya yana da alaƙa da ƙara zurfafa dangantakar ƙasar da Isra’ila.
Asali: Legit.ng
