Abin Kunya: An Kama Matar Aure kan Yanayin Yadda Saurayinta Ya Mutu a Ɗakin Otal

Abin Kunya: An Kama Matar Aure kan Yanayin Yadda Saurayinta Ya Mutu a Ɗakin Otal

  • Rundunar ’yan sandan Abuja ta kama matar aure, Rukayat Muhammed kan zargin hannu a mutuwar wani mutum a Gwarimpa
  • An gano gawar mamacin, wanda ake zargin saurayin matar auren ne a gefen titin Kubwa a Katampe
  • ’Yan sanda sun ce har yanzu suna ci gaba da binciken musabbabin mutuwar matashin kafin daukar mataki na gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Rundunar ’Yan Sandan Abuja ta kama wata matar aure, Rukayat Muhammed, kan zargin hannu a mutuwar wani mutum da ake zargin masoyinta ne a wani otal da ke Gwarimpa, Abuja.

Kwamishinan ’Yan Sandan Abuja, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ne ya bayyana hakan yau Asabar yayin da yake yi wa manema labarai bayani a hedikwatar rundunar da ke Abuja.

Yan Sanda.
Dakarun hukumar yan sanda ta Najeriya a bakin aiki Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

A rahoton Leadership, Sanusi ya ce iyalan mamacin, wanda ba a bayyana sunansa ba, sun fara kai rahoton bacewarsa kafin daga bisani aka gano gawarsa a gefen titin Kubwa kusa da gadar da ke Katampe a ranar 26 ga Agusta, 2026.

Kara karanta wannan

Duk da sulhun da gwamna ya yi, Fulani sun bi dare sun yi wa mutane kisan rashin imani

Yan sanda sun gudanar da bincike

A cewar kwamishinan, gano gawar ya haifar da rahotanni da hasashe da ke alakanta mutuwar da satar mutane ko kuma fashi da makami.

Sai dai binciken ’yan sanda ya tabbatar da cewa mamacin shi ne mutumin da iyalansa suka kai rahoton bacewarsa tun farko.

CP Sanusi ya ce masu bincike sun gano cewa wayar mamacin ta ɓace, lamarin da ya sa suka fara ƙoƙarin bin diddigin wayar da kuma gano mutanen da ya yi magana da su na ƙarshe.

Ko da yake daga baya an kashe wayar, masu binciken sun gano mutumin da mamacin ya yi magana da shi na ƙarshe, lamarin da ya kai su ga cafke Rukayat Muhammed da ke Garki Area 2.

An gano alaƙarsa da Rukayat

Sanusi ya ce ƙarin bincike ya nuna cewa wadda ake zargin matar aure ce kuma ana zargin tana da alaƙar soyayya da mamacin, inda ta ajiye lambarsa a wayarta da sunan “Safiyat”.

Kara karanta wannan

Bayan kwanaki 61, an ceto shugaban ƙaramar hukumar da ya fada tarkon yan bindiga

Ya bayyana cewa binciken ya kuma gano cewa Rukayat da mamacin sun sauka a Good Samaritan Guest House da ke 2nd Avenue, Gwarimpa, inda suka kwashe wani lokaci tare.

A cewar kwamishinan, wadda ake zargin ta shaida wa masu bincike cewa ta gano mamacin ba ya numfashi kuma ya mutu.

Sanusi ya ce:

“Maimakon ta kai rahoton lamarin ga ’yan sanda nan take, wadda ake zargin ta ɗauki wayar mamacin sannan ta bar otal ɗin.”

Yadda aka jefar da gawar saurayin

Ya bayyana cewa bayan wasu sa’o’i, lokacin da ma’aikatan gidan saukar baƙin suka kasa samun damar tuntuɓar mutanen da ke ɗakin, sai aka shiga ɗakin, inda aka gano gawar mamacin.

CP Sanusi ya ce maimakon su kai rahoton gawar ga ’yan sanda, wasu ma’aikatan gidan saukar baƙin biyu, Ibrahim Omeiza da Kefat Bitrus, sun fitar da gawar daga ɗakin.

Abuja.
Tswirar babban birnin tarayya Abuja Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ya ce daga nan suka kai gawar zuwa Kubwa kusa da gadar Katampe, inda suka jefar da ita a gefen hanya, domin nisanta otal ɗin da masu gudanar da shi daga lamarin.

Sanusi ya ce binciken ’yan sanda ya gano wani muhimmin ɓangare na abubuwan da suka faru kafin gano gawar, amma ya jaddada cewa har yanzu ana ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Farashin mai ya ruguzo kasa bayan Trump da Iran sun fahimci juna

Matar aure ta kashe mijinta a Kano

Kun ji cewa rahotanni sun nuna cewa an kama wata matar aure, Bilkisu Sani a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano kan zargin kashe mijinta, Hafizu Gausu.

An ruwaito cewa marigayin na shirin kara auren wata mata a matsayin matarsa ta biyu, wanda hakan ya fusata uwargidansa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262