Fin Karfi: Ana Zargin Kwamishina Ya Raba Aure, Ya Lallaba Ya Auri Matar a Zamfara
- Wani magidanci ya zargi Kwamishinan Hisbah na dindindin a Zamfara da amfani da matsayinsa wajen tilasta rabuwar aurensa
- Mai ƙarar ya ce Kwamishinan, Faruk Dandalin Faila, daga baya ya auri tsohuwar matarsa Aisha bayan an raba aurensu
- Ya kuma nemi gwamnatin Zamfara ta gudanar da bincike da kuma yadda ’ya’yansa biyu suka shiga hannun Sirajo Kwaren Ganuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Wani magidanci a Zamfara ya shigar da ƙorafi ga gwamnatin jihar, yana zargin wani babban jami’in Hisbah da tsoma baki cikin aurensa.
A cikin ƙorafin mai kwanan wata 26 ga Agusta, 2026, magidancin ya zargi Faruk Dandalin Faila Kaura Namoda da Sirajo Kwaren Ganuwa.

Source: Original
Yadda Hisbah ta raba aurensu a Zamfara
Ya ce mutanen biyu sun shiga tsakani a rikicin aurensa da Aisha, amma a cewarsa, sasancin ya koma matsin lamba, cewar Aminiya.
Magidancin ya yi zargin cewa daga baya Faruk Dandalin Faila ya auri Aisha, bayan an samu rabuwar aurensu.
Ya kuma buƙaci a binciki ko jami’an sun yi amfani da mukamansu ko tasirinsu wajen tsoma baki cikin rikicin.
Wani ɓangare na ƙorafin ya shafi ’ya’yansa biyu, inda ya ce a yanzu suna ƙarƙashin kulawar Sirajo Kwaren Ganuwa.
Magidancin ya nemi a binciki yadda yaran suka shiga hannun Ganuwa da kuma ko akwai wata hujjar doka.
Ya kuma nuna damuwa kan yiwuwar amfani da matsayi, tsoratarwa ko matsin lamba wajen hana shi samun damar kula da ’ya’yansa.

Source: Facebook
Rokon magidancin ga gwamnatin Zamfara
Magidancin ya roƙi gwamnati ta binciki yadda auren Faruk Dandalin Faila da tsohuwar matarsa ya gudana bayan rabuwar aurensu.
Ya ce binciken zai taimaka wajen gano ko an samu rashin da’a ko kuma amfani da matsayi wajen cimma wani buri.
Sai dai Sirajo Kwaren Ganuwa ya musanta zarge-zargen, yana mai cewa yana da kyakkyawar alaƙa da magidancin.

Kara karanta wannan
Yan bindiga sun shiga fadar Sarki, sun kashe shi bayan korafi kan ta'adinsu a Niger
Ganuwa ya bayyana cewa ya shiga lamarin ne a matsayinsa na babban ɗan uwa ga Aisha, ba a matsayin jami’in gwamnati ba.
Ya ce sau da dama ya ƙarfafa Aisha ta koma gidan mijinta, duk da cewa tana da wasu ƙorafe-ƙorafe.
Ganuwa ya kuma musanta cewa ya hana mahaifin yaran ganinsu, amma ya ce ba za su amince ya ɗauke su na dindindin ba.
A cewarsa, hakan ya faru ne saboda yana ganin mahaifin ba shi da aure kuma ba zai iya kula da yaran yadda ya dace ba.
A halin yanzu, shugaban Hukumar Hisbah ta Zamfara, Umar Hassan Gusau, bai mayar da martani kan zarge-zargen ba.
An ce an tuntube shi ta waya, SMS da WhatsApp domin jin matsayinsa, amma bai amsa ba har lokacin kammala rahoton.
Magidancin ya ce yana da takardu, saƙonni da wasu hujjoji da zai gabatar idan gwamnati ta fara bincike kan lamarin.
Ya kuma nemi a kare shi da kuma kiyaye sirrinsa saboda fargabar yiwuwar tsoratarwa ko ramuwar gayya.
Daga cikin buƙatunsa akwai tabbatar da karɓar ƙorafinsa da tura zarge-zargen ga hukumomin da suka dace domin gudanar da bincike.
Hisbah ta kama ma'aurata kan saba ka'ida
An ji cewa Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama matasa biyar bisa zargin yin aure ba tare da amincewar iyaye ba.
Rahoto ya ce cikin wadanda aka kama akwai amarya, ango, da wasu uku da suka shiga wajen shaidar aure.
Hisbah ta byyana cewa an yi auren ne da sadaki na ₦10,000 wanda bai kai ka’idar da Musulunci ya tanada ba.
Asali: Legit.ng

