Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Shugaban APC a Kano

Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Hallaka Shugaban APC a Kano

  • Yan bindiga dauke da makamai sun kai wani harin da ya yi sanadiyyar rasa ran wani shugaban jam'iyyar APC a jihar Kano
  • Maharan sun kuma kashe Sulaiman Zunduma nan take bayan sun kai wa mazauna Rantan hari da daren Lahadi
  • Harin ya zo ne sa’o’i bayan an ceto Sarkin Noman Kano, Yusuf Nadabo Chiromawa, wanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kai hari kauyen Rantan da ke ƙaramar hukumar Bebeji ta Jihar Kano, inda suka kashe mutane biyu.

Daga cikin waɗanda aka kashe akwai shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na mazabar Rantan, Alhaji Garba Buba.

'Yan bindiga sun kashe shugaban APC a Kano
Taswirar jihar Kano, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Wani mazaunin yankin, Hamza Isah Rantan, ya tabbatar da harin a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, inda ya yi ta’aziyyar waɗanda lamarin ya rutsa da su.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari Kano, an sace babban mai rike da sarauta da kashe mutane

Shugaban APC ya mutu a asibiti

Hamza ya bayyana cewa maharan sun harbi Buba yayin da suke kai hari a garin a daren Lahadi, 30 ga watan Agustan 2026.

A cewarsa, an garzaya da shugaban na APC zuwa asibiti domin samun magani, amma daga bisani ya rasu sakamakon raunukan da ya samu.

Ya kuma ce Sulaiman Zunduma, wanda maharan suka harba a yayin harin, ya mutu nan take.

Hamza ya rubuta cewa:

"A daren Jiya Lahadi masu garkuwa da mutane suka kawo farmaki a garinmu na Rantan inda suka harbi Alh Garba Buba shugaban jam'iyyar APC na mazabar Rantan wanda hakan yayi sanadiyyar rasuwarsa bayan an kai shi asibiti da Alh Sa'adu da kuma kashe mutum daya wato Sulaiman Zunduma."
"Muna addu'ar Allah ya ba su lafiya Ya kuma kiyaye gaba shi kuma Ubangiji Ya ji kansa yayi masa Rahama Ya sa aljannace makomarsa Ya bawa ahali juriyar rashinsa."

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun harbe shugaban jam'iyyar APC, sun tafi da mutumin da suke tare

"Ubangiji Ya kubutar da wadanda suke hannunsu yayi mana tsari daga sharrin mutanen Nan Ya kawo mana dauki albarkacin Shugaba Annabi Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama Ameen Ya Hayyu Ya Qayyum"

Harin ya biyo bayan sace Sarkin Noma

Sabon harin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan ceto Sarkin Noman Jihar Kano, Alhaji Yusuf Nadabo Chiromawa, wanda wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a garin Chiromawa da ke ƙaramar hukumar Garun Malam.

A harin da aka kai Chiromawa da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Asabar, ’yan bindiga sun kai farmaki gidan Sarkin Noman tare da buɗe wuta kan mutane.

’Yan sanda ba su yi bayani ba

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, rundunar ’yan sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan sabon harin na Rantan ba.

Hare-haren da suka faru a Rantan da Chiromawa, waɗanda ke kusa da juna, sun ƙara jefa mazauna yankin cikin fargaba tare da ƙara matsin lamba kan hukumomin tsaro da su ƙara ƙoƙarin kare al’ummomin yankunan.

'Yan bindiga sun kai hari a Kano
Kwamishinan 'yan sandan jihar Kano, CP Ibrahim Bakori Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

'Yan bindiga sun sace matafiya

A wani labarin kuma, kun ji cewa matafiya da-dama ake tunanin miyagun ‘yan bindiga sun yi awon gaba da su sakamakon wani hari da aka kai a jihar Zamfara.

An sace mutanen ne bayan 'yan bindiga sun tare hanyar Gusau zuwa Funtua, a daidai daf da shiga garin Tsafe, karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng