Betta Edo da Wasu Gingima Gingima da Ake Zargi da Aka Gano cikin Kamfen Tinubu
- An saka tsohuwar ministar jin ƙai Betta Edu da wasu da ake zargi da badakala a Najeriya cikin kwamitin yaƙin neman zaben APC na 2027
- Betta Edu za ta kasance daraktar wayar da kan mata, Ngozi Olejeme za ta jagoranci shirye-shiryen zaɓe da haɗa kai a Kudu maso Kudu
- Edu ta fuskanci binciken EFCC, yayin da Olejeme ke fuskantar shari’ar zargin karkatar da Naira biliyan 1
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - An saka tsohuwar ministar jin ƙai da yaƙi da talauci, Betta Edu, cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na 2027.
Haka kuma, an saka tsohuwar shugabar hukumar NSITF, Ngozi Olejeme, cikin kwamitin da jam’iyyar ta bayyana ranar Asabar.

Source: Twitter
Betta Edu ta shiga jerin masu kamfen Tinubu
Edu, wadda ke lamba 97 a jerin sunayen, an naɗa ta daraktar wayar da kan mata a kwamitin yaƙin neman zaɓen, cewar TheCable.
Olejeme kuwa, wadda ke lamba 37, za ta kasance daraktar shiyyar Kudu maso Kudu mai kula da tsare-tsaren zaɓe, haɗin kai da wayar da kan jama’a.
A cikin shekarun baya, an danganta matan biyu da zarge-zargen almundahana, waɗanda suka gabaci cire su daga mukaman da suke riƙe da su.
A ranar 8 ga Janairu, 2024, Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Betta Edu daga mukamin ministar jin ƙai.
Hakan ya biyo bayan wani takarda da ta bayyana cewa Edu ta nemi Akanta-Janar na Tarayya, Oluwatoyin Madein, ya tura N585 miliyan zuwa wani asusun banki mai zaman kansa.
Daga bisani, Shugaban ƙasar ya dakatar da dukkan shirye-shiryen da Hukumar NSIPA ke gudanarwa na tsawon makonni shida domin gudanar da bincike
A watan Afrilun 2024, EFCC ta ce ta kwato N30 biliyan bayan binciken ayyukan ma’aikatar, tare da bayyana cewa ana binciken asusun banki 50.
Har zuwa lokacin da aka wallafa rahoton, EFCC ba ta bayyana rahoton binciken da ta gudanar kan tsohuwar ministar ba.

Source: UGC
Shari’ar Olejeme kan zargin almundahana
A watan Oktoban 2025, EFCC ta gurfanar da Ngozi Olejeme a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan zargin halasta kuɗin haram na Naira biliyan 1.
An tuhume ta da laifuka takwas da suka shafi mayarwa, tura, samo da kuma mallakar kuɗaɗen da ake zargin an samu ta hanyar haram.
EFCC ta ce Olejeme ta karkatar da wasu kuɗaɗen hukumar NSITF tsakanin shekarun 2012 da 2015, lokacin da take shugabar hukumar, cewar Punch.
Olejeme ta musanta dukkan zarge-zargen, yayin da lauyan EFCC, Emenike Mgbemele, ya nemi kotu ta sanya ranar fara sauraron shari’ar.
Jerin mutane 108 da aka saka a kamfen Tinubu
An ji cewa Shugaba Bola Tinubu ne shugaban Kwamitin Yakin Neman Zaɓen APC na 2027, yayin da Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ke cikin tafiyar.
An naɗa tsohon gwamnan Zamfara, Sanata Abdulaziz Yari, a matsayin Darakta Janar na kwamitin, yayin da Gwamnan Imo, Hope Uzodimma, ya zama sakataren kwamitin.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ne ya fitar da jerin sunayen mambobin kwamitin a wata sanarwa ranar Asabar.
Asali: Legit.ng

