'Yan Ta'addan ISWAP Sun Gamu da Mummunan Bala'i bayan Kai Hari a Borno
- ’Yan ta’addan ISWAP sun kai hari kan sansanin sojoji a Kukawa daga wurare huɗu, amma dakarun Najeriya sun yi nasarar fatattakarsu
- Majiyoyin tsaro sun ce an kashe fiye da ’yan ta’addan 25, yayin da sojoji suka gano gawarwaki 14 a filin daga
- ’Yan ta’addan sun bar makamai da alburusai, ciki har da bindigogin AK-47 guda shida, yayin da sojojin Najeriya ma suka samu asarar rayuka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Borno - Dakarun Bataliya ta 101 ta Musamman ta Sojojin Najeriya da ke Kukawa, Jihar Borno, sun yi nasarar fatattakar wani babban hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansaninsu.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun kai harin ne daga wurare huɗu daban-daban, a wani yunƙuri na mamaye sansanin sojojin.

Source: Original
An shafe kusan sa’o’i uku ana musayar wuta

Kara karanta wannan
Zance ya kare: INEC ta yi magana kan hukuncin kotu da zai iya shafar takarar su Pantami
Majiyoyin tsaro sun shaida wa jaridar Vanguard cewa harin ya faru ne tsakanin ƙarfe 9:00 na dare zuwa 11:30 na dare ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026.
An ce ’yan ta’addan da dama sun kai wa sansanin hari cikin haɗin gwiwa, lamarin da ya janyo musayar wuta mai tsanani tsakanin bangarorin biyu.
Dakarun sojin, tare da tallafin rundunar sojin sama, sun mayar da martani tare da fatattakar ’yan ta’addan bayan shafe lokaci ana gwabza faɗa.
An kashe fiye da ’yan ta’adda 25
Majiyoyin sun ce ’yan ta’addan sun yi asarar rayuka masu yawa, inda aka kashe fiye da 25 daga cikinsu.
Ya zuwa yanzu, sojojin sun gano gawarwakin ’yan ta’adda 14 a filin daga, yayin da wasu daga cikin maharan suka tsere daga yankin bayan fatattakarsu.
An kuma ce sojojin sun kwato makamai da alburusai masu yawa da ’yan ta’addan suka bari a lokacin da suke gudu. Daga cikin makaman da aka kwato akwai bindigogin AK-47 guda shida.
Sojoji ma sun samu asarar rayuka
Duk da nasarar da sojojin suka samu wajen dakile harin, majiyoyin sun ce rundunar sojin ma ta samu asarar rayuka a yayin mummunan arangamar.
Wasu sojoji sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka samu raunuka a lokacin musayar wutar.
Bayan fatattakar harin, Kwamandan Brigade ya isa yankin domin jagorantar sake tsara dabarun kare sansanin.
An kuma ce ya jagoranci matakan ƙara yawan dakarun da ke yankin, da samar da kayan aiki, tare da ci gaba da binciken filin daga domin gano ƙarin bayanai da makamai.
Kwamandan Operation Hadin Kai ya tabbatar da harin
Kwamandan Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation Hadin Kai, Manjo Janar Ibikunle Ajose, ya tabbatar da cewa an kai hari kan sansanin sojojin da ke Kukawa.
A cikin gajeren saƙonsa, ya ce:
“Eh, wasu ’yan ta’adda sun kai hari sansaninmu da ke Kukawa, amma an fatattake su. Sun yi asarar rayuka masu yawa.”

Source: Twitter
'Yan Boko Haram sun kashe kwamanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa yan ta’addan Boko Haram da ISWAP ne sun kai wani mummunan hari kan al’ummar Wumbi da ke ƙaramar hukumar Kala-Balge a Jihar Borno.
Rahotanni sun ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar wani kwamandan ’yan sa-kai da fararen hula huɗu, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
Asali: Legit.ng
