An Lalubo Gwamna 1 da Zai Iya Maye Gurbin Bola Tinubu a Zaben 2027
- Jam'iyyar APM ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na Makinde/Daura a Abuja ranar Talata da ta gabata
- A wurin taron, Darakta Janar na kwamitin, Felix Hyat ya ce lokaci ya yi da yan Najeriya su canza shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu
- Ya bayyana Gwamna Makinde na jihar Oyo a matsayin wanda ya cancanta ya maye gurbin Tinubu a babban zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Makinde-Daura, Felix Hyat, ya gargadi ’yan Najeriya, musamman matasa a Arewa, da kada su zaɓi Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Fellix Hyat ya bukaci matasan Najeriya da su maye gurbinsa da ɗan takarar shugaban kasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, wanda shi ma ɗan Kudu maso Yamma ne.

Kara karanta wannan
'Dan takarar shugaban ƙasa ya cika baki, ya ce zai samu ƙuri'u kusan miliyan 70 a zaben 2027

Source: Facebook
Premium Times ta rahoto cewa Mista Hyat ya bayyana hakan ne ranar Talata a Abuja yayin ƙaddamar da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na Makinde-Daura na jam'iyyar APM a Abuja.
APM ta soki matasan Arewa
Ya kuma soki matasan Arewa kan ci gaba da goyon bayan ’yan siyasar da ke neman shugabancin ƙasa, yayin da ake barin matasa masu neman kujerar a baya.
Ya ce duk wani ɗan Najeriya yana da ’yancin kundin tsarin mulki na neman duk wata kujerar siyasa, amma matasan Arewa ya kamata su tambayi kansu ko ci gaba da goyon bayan tsofaffin ’yan siyasa na amfanar da su.
“Babu shakka kowa yana da ’yancin neman kowace irin kujera. Amma don Allah, matasan Arewa masu basira, kuzari da himma, za su nade hannayensu su bar mutum guda ya yi ta yin talara, su kuma su ci gaba da jira har su tsufa? Hakan na nufin ba ku da makoma,” in ji shi.
Mista Hyat ya ce tun da Tinubu, wanda ya fito daga Kudu maso Yamma, ya fara wa’adinsa na farko na shekaru huɗu, ya kamata Arewa ta bar ɗan kudu ta kammala wa’adin shekaru takwas.
APM ta tallata Makinde ga yan Najeriya
Ya kuma kalubalanci Kudu maso Gabas, wadda ya ce tana neman samun shekaru huɗu na shugabancin ƙasa, da ta dawo ta yi la’akari da burin matasan ’yan siyasa daga yankin.
Mista Hyat ya ce gwamnatin APC ta gaza wajen yi wa ’yan Najeriya abin da suke bukata duk da cewa ta samar da shugaban ƙasa daga Kudu maso Yamma.
Ya kara cewa mafita ba ita ce a ƙi yankin ba, sai dai a maye gurbin Bola Tinubu da wani ɗan takara daga yankin, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Source: Twitter
Ya bayyana Gwamna Makinde da ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na APM, Lawal Daura, a matsayin ’yan siyasa da aka gwada, wadanda za su iya magance matsalar rashin tsaro da sauran ƙalubalen da Najeriya ke fuskanta.
Mista Hyat ya ce yaƙin neman zaɓen ba wai kawai wani aikin siyasa ba ne, illa dai nauyi ne da ya rataya kan ’yan Najeriya domin kare makomar matass masu zuwa.

Kara karanta wannan
Tsohon ɗan Majalisa ya bukaci Atiku da Peter Obi su janyewa Tinubu, ya kawo hujja
Makinde na hangen nasara a 2027
Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya ce jam’iyyarsa na shirin samun aƙalla kashi biyu bisa uku na ƙuri’un masu zaɓe miliyan 103.
Gwamna na jihar Oyo a ce yaƙin neman zaɓensa zai gudana ne bisa tanadin Dokar Zaɓe ta 2026 domin samun nasara a zaben 2027.
Asali: Legit.ng
