‘Abin da Ya Sa Nyesom Wike Bai Zama Darakta Janar na Kamfen Tinubu ba’

‘Abin da Ya Sa Nyesom Wike Bai Zama Darakta Janar na Kamfen Tinubu ba’

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana bayan APC ta fitar da kwamitin kamfen shugaban kasa na Shugaba Bola Tinubu a 2027
  • Wike ya bayyana cewa wasu tsofaffin daraktocin kamfen sun taimaka wa ‘yan takararsu, amma daga baya suka rasa jihohinsu
  • Ya ce zai fi mayar da hankali wajen tabbatar da nasarar Tinubu a Abuja da Rivers, yana mai cewa sakamako ya fi mukamin kamfen muhimmanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai iya zama Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaba Bola Tinubu na 2027 ba.

Tsohon gwamnan Rivers wanda yanzu shi ne ministan Abuja ya tabbatar da cewa hakan ba zai yiwu ba saboda ba ɗan APC ba ne.

Wike ya magantu kan kwamitin kamfen APC
Ministan Abuja, Nyesom Wike da Shugaba Bola Tinubu a Abuja. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Ya bayyana hakan ne bayan duba ayyukan hanyar Apo-Karshi da Kubwa-Bwari a Abuja, inda ya ce aikin zai kammala kafin ƙarshen shekarar nan, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Minista ya fasa kwai, an ji yadda ake shirin ƙarawa Atiku 'hawan jini' kafin zaben 2027

Wike ya magantu kan zama darakta-janar

Wike ya ce baya son shiga cikin jerin tsofaffin daraktocin kamfen da suka yi ƙoƙarin lashe zaɓe, amma suka rasa jihohinsu, kamar Rotimi Amaechi, Bukola Saraki, Aminu Waziri Tambuwal da Simon Lalong.

Da aka tambaye shi ko yana son kasancewa cikin majalisar yaƙin neman zaɓen APC, Wike ya ce ba ya buƙatar shiga tsarin APC domin tallafa wa Tinubu.

Ya ce lokacin da yake yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2023, shi da abokansa ba sa cikin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC.

Wike ya ce sun yi amfani da dabarunsu wajen taimakawa Tinubu ya samu nasara, yana mai cewa irin wannan tsarin ne suke ci gaba da amfani da shi.

Ya bayyana cewa “Rainbow Coalition” ta ƙunshi ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da ke aiki tare domin tabbatar da nasarar Tinubu a jihohinsu.

Ya ce haɗin gwiwar na aiki a wasu jihohi, ciki har da Kwara, Bayelsa, Rivers, Osun da Benue, inda ’yan siyasa ke goyon bayan Tinubu.

Kara karanta wannan

Malamin addini da ke goyon bayan Tinubu ya magantu kan tallafin mai

APC ta fitar da kwamitin kamfen zaben Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yayin taro a Abuja. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Source: Facebook

'Abin da ya kamata ga dan siyasa'

Wike ya jaddada cewa ba mukamin Daraktan Kamfen ne ya kamata a yi amfani da shi wajen auna tasirin ɗan siyasa ba, sai sakamakon da ya samar.

Ya ce babban burinsa shi ne tabbatar da nasarar Tinubu a FCT da Rivers, yana mai cewa yana kallon waɗannan wurare a matsayin “jihohinsa biyu”.

Wike ya ce:

“Ba na son rasa jihata! Zan kasance a jihata. Ina da jihohi biyu: Abuja da Rivers. Muhimmin abu shi ne nasarar waɗannan jihohin biyu.”

Ya ƙara da cewa idan mutum Daraktan Kamfen ne amma bai iya lashe jiharsa ba, babu wata fa’ida mai yawa da mukamin zai kasance da ita.

Dangane da rashin kasancewarsa ɗan APC, Wike ya ce hakan ya sa batun shugabantar Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa ta APC bai shafe shi ba.

Wike ya kuma ce babu wanda ya kamata ya yi amfani da kasancewa cikin Majalisar Kamfen wajen tantance wanda zai zama gwamna, domin sakamakon zaɓe ne zai tabbatar.

Kara karanta wannan

Gombe 2027: Sakon Jamilu Gwamna ga Pantami, ADC ana daf da fara kamfen

Wike ya roki yan Abuja kan zaben sanata

An ji cewa Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi magana game da zaben 2027 musamman na sanatoci a shekara mai zuwa.

Wike ya bukaci mazauna Abuja su ki sake zaben Sanata Ireti Kingibe, yana mai neman su zabi tsohon Sanata Philip Aduda a 2027.

Ministan ya ce Aduda “mutumin jama’a” ne mai kwarewar wakiltar bukatun mazauna Abuja, yayin da ya zargi Kingibe da rashin ziyartar al’ummomi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.