Yadda Hukumar Bogi Ta Yi Ta Yaudarar Gwamnoni Tana Neman Kudi da Filaye
- ICPC ta gano hukumar bogi da ta rika aika wa gwamnonin jihohi takardun neman tallafi da gudumuwa
- Hukumar ta yi amfani da sunan 'Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya' wajen neman kudin taro a kasashen waje
- Nwabueze George ya nemi wasu gwamnoni su bada hadin-kai a shirya taron kaddamar da jagororin jihohi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Abuja - An bankado wata hukumar bogi a Najeriya, hakan ya sa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da wasu manyan jami’ai uku.
Wannan ya sa aka shiga bincike game da wannan ofishi na musamman da aka ce an kikira domin a rika amfani da kayan gida.

Source: Facebook
Bincike kan ayyukan hukumar bogi
Jaridar Premium Times ta fitar da rahoto na musamman game da wannan hukuma da aka ce shugaban kasa bai san da zaman ta ba.
Binciken ya nuna cewa hukumar ta rika amfani da takarda daga ofishin sakataren gwamnati da tambarin fadar shugaban kasa.
Wadannan takardu aka rika aika wa jihohi wajen daukar mutane aiki, neman kudi, gayyata zuwa taro, rokon filaye da makamantansu.
Wasikun da hukumar ta tura wa gwamnoni
A farkon shekarar nan, hukumar ta rubuta wasika zuwa ga gwamnonin Legas, Imo, Ondo, Edo, Sokoto da kuma na Nasarawa.
Takardun sun roki gwamnatocin jihohin su taimaka da kudi da filaye domin yin wasu ayyuka a gida Najeriya da kasashen waje.
Nwabueze George ya sa hannu a duk irin wadannan takardu da sunan shi a matsayin shugaba kuma jagoran hukumar ta kasa.
Abin da aka fada wa gwamnonin shi ne gwamnatin tarayya za ta hada-kai da jihohi wajen taimaka wa kananan ‘yan kasuwa.
An kuma ce za a yi tarayya wajen farfado da masana’antu da kasuwanci da kasashen ketare.
Takardu zuwa ga gwamnonin Legas, Edo da wasu jihohi
A ranar 9 ga Junairu ya rubuta wa Babajide Sanwo-Olu takarda ya neman ya zabi wanda zai jagoranci aikinsu a jihar Legas.
Ita gwamnatin jihar Edo kuwa cewa aka yi ta taimaka da kudi da za a halarci wani taro a kasar Bahrain, za a yi wa jami’ai rajista.
Kudin rajistar kowane jami’i zai ci $2500, don haka aka nemi $75, 000 domin mutane 30.
Da aka tuntubi gwamnatin Nasarawa, an roki Abdullahi Sule ya bada gudumuwarsa wajen yin taron masu ruwa da tsaki.
An shirya taron ne a garin Lafia tsakanin 28 zuwa 30 ga watan Afrilu 2026. A nan aka so a kaddamar da shugabannin hukumar.
Da aka je Ondo kuwa, hukumar bogin ta roki Mai girma Lucky Aiyedatiwa ya taimaka da fili domin a iya kafa ofishi a jihar.
Gwamnonin Imo da Sokoto ba su sha ba
A Imo, an aika wa Hope Uzodimma takarda ana neman ya zama babban mai jawabi a taro na kasan da za a yi a babban birnin Nasarawa.
Ban da kasancewarsa mai jawabi, an kuma roki Gwamnan Imo ya bada kudin otel, cin abinci, shirya taro, rajista da na zirga-zirga.

Source: Getty Images
Hukumar ta gayaci Gwamnan Sokoto ya halarci wani taron harkar noma da aka shirya za a yi a kasashen Bahrain da Azerbaijan.
Akwai gayyatar da aka tura wa wasu jihohin zuwa wasu taron a Burundi, Equatorial Guinea, China, South Korea da kasar Oman.
Annobar hukumomin bogi a cikin gwamnatin Najeriya
An ji labari ICPC ta wanke Fadar Shugaban Kasa daga zargin kafa hukumar bogi ta PFIPC ko nada Adeniyi Adeyemi a matsayin shugabanta.
Binciken ICPC ya nuna dukkan takardun nadin da Adeyemi ya yi amfani da su na jabu ne, sannan kuma gwamnati ba ta taba ba shi kudi ba.
Baya da PFIPC, ICPC ta gano cewa Adeyemi ya taba amfani da irin wannan hanyar ta damfara wajen kirkirar wasu hukumomin bogi a baya.
Asali: Legit.ng


