EFCC: Babban kotun tarayya ta bada umarni a karbe wasu gidajen Ngozi Olejeme

EFCC: Babban kotun tarayya ta bada umarni a karbe wasu gidajen Ngozi Olejeme

A ranar Laraba, 1 ga watan Yuli, 2020, Alkali Taiwo Taiwo na babban kotun tarayya da ke Abuja ya bada umarnin a soma karbe wasu gidaje da kadarori na Misis Ngozi Olejeme.

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta na zargin Ngozi Olejeme wanda ta rike hukumar NSITF da laifin satar dukiyar gwamnati.

Gidajen da Alkali ya bada damar a fara karbewa daga hannun tsohuwar shugabar ta NSITF sun kai 48. Hukumar EFCC ta bayyana mana wannan a shafinta na Twitter a ranar Laraba.

Wadannan dukiyoyi da ake zargi an mallake su da dukiyar sata su na rarrabe ne a manyan garuruwan Kudancin Najeriya irinsu: Bayelsa, Enugu, Edo, Delta da kuma babban birnin tarayya Abuja.

Bayan rike hukumar NSITF mai kula da dukiyar da aka ware domin jin dadin ma’aikatan gwamnatin tarayya, Olejeme ta na cikin manyan jam’iyyar PDP a gwamnatin Goodluck Jonathan.

KU KARANTA: Dole a gyara yadda ake dankare mutane a gidajen yari - Sanata Kalu

EFCC: Babban kotun tarayya ta bada umarni a karbe wasu gidajen Ngozi Olejeme
Ngozi Olejeme Hoto: This Day
Asali: Instagram

Ngozi Olejeme ta kasance ma’aji na kwamitin yakin neman zaben Jonathan-Sambo a 2015.

Tun a shekarar 2016, hukumar EFCC ta ke farautar Ngozi Olejeme, inda a Satumban 2017, hukumar ta yi shelar cewa ta na neman tsohuwar jami’ar gwamnatin kasar.

EFCC ta na zargin Ngozi Olejeme da wani Umar Munir Abubakar da laifuffukan da su ka hada da cin amanar aiki, satar dukiyar kasa da karkatar da akalla Naira Biliyan 69 daga asusun gwamnati.

Lauyan EFCC Ekele Iheanacho ya gamsar da Alkali cewa Olejeme ta mallaki wadannan kadarori ne da kudin haram. Lauyan ya iya gabatar da manyan hujjoji har 14 a gaban kotu.

Mai shari’a Taiwo Taiwo ya yi na’am da bukatar EFCC, ya ce hukumar ta rike dukiyoyin har zuwa nan da lokacin da za a ji ko za a maida kadarorin hannun gwamnatin tarayya na din-din-din.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel