Trump Ya Yarda za a Harbe Tsohon Sojan Amurka a gaban Jama'a

Trump Ya Yarda za a Harbe Tsohon Sojan Amurka a gaban Jama'a

  • Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da cewa za a kashe tsohon kwararren likitan sojan Amurka, Nidal Malik Hasan, ta hanyar harbe shi
  • Matakin shi ne irinsa na farko da sojojin kasar za su dauka tun bayan yakin duniya na biyu fiye da shekaru 60 da suka gabata
  • Hasan ya aikata kisan gillar ne a cibiyar sojoji ta Fort Hood a shekarar 2009 inda ya kashe sojoji 13 sannan ya raunata mutum 32

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington DC – Ma'aikatar tsaron Amurka ta sanar da shirin kashe wani tsohon ma'aikacin rundunar sojin kasar ta hanyar amfani da masu harbi.

Wanda abin ya shafa shi ne Nidal Malik Hasan, tsohon manjo kuma kwararren likitan kwakwalwa na sojan Amurka, wanda aka samu da laifin kashe sojoji 13 tare da raunata wasu 32 a sansanin Fort Hood da ke jihar Texas a shekarar 2009.

Kara karanta wannan

An saki sunayen sojoji da mutum 25 da suka rasu a hadarin jirgin soji a Ondo

Donald Trump da Nidal Malik Hasan
Donald Trump a hagu da Nidal Malik Hasan a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

BBC ta rahoto cewa magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka, Sean Parnell, ya tabbatar da cewa Sakataren Yaki Pete Hegseth ne ya mika shawarar, yayin da Shugaba Donald Trump ya amince da ita.

Za a harbe tsohon sojan Amurka

A bayanan da Parnell ya bayyana a shafinsa na X game da cewa za a kashe Hassan a bainar jama'a, ya wallafa cewa:

"Ranar sakayya ga Hasan ta zo."

Ya kara da cewa ministan rundunar sojin ne zai kayyade lokaci da kuma wurin da za a aiwatar da hukuncin.

A yayin shari'arsa a kotun soji a shekarar 2013, Hasan ya amsa laifinsa na kasancewa mai harbin, inda ya bayyana cewa ya aikata hakan ne domin kare mambobin kungiyar Taliban da Musulmai a kasar Afghanistan.

Wannan hari na ranar 5 ga Nuwamba, 2009 shi ne hari mafi muni da aka taba kaiwa a cikin sansanin sojin Amurka wanda ba na yakin gaba da gaba ba.

Kara karanta wannan

Shettima ya dura jihar Katsina, an raba miliyoyin Naira kyauta

Dokokin hukuncin kisa a Amurka

A karkashin dokar soji ta Amurka, amincewar shugaban kasa ita ce matakin karshe na aiwatar da hukuncin kisa ga sojan da aka samu da laifi.

Donald Trump ya sake maida amfani da hukuncin kisa a matakin gwamnatin tarayya ta hanyar wata doka ta musamman da ya rataba wa hannu a Janairun 2025, bayan ma'aikatar shari'a karkashin tsohon shugaba Joe Biden ta dakatar da amfani da shi.

Sojojin Amurka a kasar su
Sojojin Amurka sun dauko sojan da aka kashe a yakin Iran. Hoto: JD Vance
Source: Facebook

Wannan shine karon farko da rundunar sojin Amurka za ta yi amfani da hanyar harbe mutum wajen aiwatar da hukuncin kisa tun bayan karshen Yakin Duniya na Biyu.

Koriya ta gwada sabon makami

A wani labarin, mun ruwaito cewa Kasar Koriya ta Arewa ta harba wani sabon tsarin makami mai linzami mai tafiya mai nisa a karkashin kulawar shugaban kasar Kim Jong Un.

Kafofin labaran kasar sun tabbatar da cewa makamin ya yi nasarar zuwa wajen da aka harba shi da ke tsakanin tazarar kilomita1,000 a cikin teku.

Gwajin ya zo ne a dai-dai lokacin da ake samun tashin hankali tsakanin Koriya ta Kudu da ta Arewa sakamakon rikicin da suka yi a kan iyakar kasashen guda biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng