Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Wani Muhimmin Nadin Shugaba Tinubu

Majalisar Dattawa Ta Tabbatar da Wani Muhimmin Nadin Shugaba Tinubu

  • Majalisar dattawa ta tabbatar da naɗin Zacch Adedeji a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS)
  • Adedeji dai ya kasance a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar ta FIRS bayan da Shugaba Bola Tinubu ya bayyana nadin sa tare da korar Muhammed Nami
  • A yayin tantancewar, Adedeji ya sha alwashin inganta ƙarfin tattara bayanai na hukumar domin samar da kuɗaɗen shigar da suka dace

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wakilin Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar fiye da shekara biyar wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum da nishaɗi

FCT, Abuja - Majalisar dattawa ƙarƙashin jagorancin Godswill Akpabio ta tabbatar da naɗin wanda shugaba Bola Tinubu ya zaba a matsayin shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS), Zacchaeus Adedeji, a ranar Talata, 31 ga watan Oktoba.

Tabbatar da Adedeji ya biyo bayan cimma matsayar hakan da mafiya yawan sanatocin suka yi. Tun da farko dai an tantance shi ne a yayin zaman majalisar a Abuja, cewar rahoton The Nation.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya yi wata hubbasa a rikicin siyasar Wike, Fubara

Majalisa ta tabbatar da nadin Adedeji
Majalisar dattawa ta tabbatar da nadin Zach Adedeji a matsayin shugaban hukumar FIRS Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Zacch Adedeji
Asali: Twitter

Adedeji ya yi alƙawarin kawo sauye-sauye a FIRS

A yayin tantancewar, shugaban riko na hukumar ta FIRS ya sha alwashin inganta tattaro bayanai na hukumar ta yadda za a iya yanke hukuncin da ya dace kan haraji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaba Tinubu ya kori Muhammad Nami, shugaban hukumar ta FIRS wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa.

Daga nan ne shugaban ƙasar ya naɗa Zacchaeus Adedeji, mai ba shi shawara na musamman kan harkokin kuɗaɗen shiga, a matsayin muƙaddashin shugaban hukumar ta FIRS.

Wanene Zacch Adedeji, shugaban FIRS?

Adedeji ya kasance tsohon kwamishinan kuɗi a ƙarƙashin marigayi Gwamna Abiola Ajimobi na jihar Oyo, muƙamin da ya riƙe yana da shekaru 33 a duniya.

Nami, wanda ake sa ran wa’adinsa zai ƙare a watan Disamban 2023, an buƙaci ya tafi hutun ritaya, yayin da Adedeji zai kasance a matsayin shugaban riƙo na hukumar.

Kara karanta wannan

Fubara da Ministan Abuja sun haɗu a Aso Villa ana ƙishin-kishin ɗin Tsige Gwamnan PDP

Adedeji ƙwararren akawu ne daga yankin Iwo-Ate da ke ƙaramar hukumar Ogo-Oluwa a jihar Oyo. A cikin ƴan kwanakin nan ya samu takardar shaidar digirin digir-gir a jami'ar Obafemi Awolowo da ke Ile-Ife a jihar Osun.

Nami na ɗaya daga cikin waɗanda tsohon shugaban ƙasa Buhari ya naɗa da Tinubu ya kora cikin watanni huɗu da hawansa mulki.

Tsohon Shugaban FIRS Ya Magantu

A wani labarin kuma, tsohon shugaban hukumar tattara haraji ta ƙasa (FIRS) Muhammad Nami, ya yi martani kan sauke shi daga muƙaminsa da Shugaba Tinubu ya yi.

Nami ya godewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da Shugaba Tinubu bisa damar da suka ba shi ya hidimtawa ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng