'Yan Sanda Sun Yi Ram da 'Yan Ta'adda 96, Sun Ceto Mutum 42

'Yan Sanda Sun Yi Ram da 'Yan Ta'adda 96, Sun Ceto Mutum 42

  • ’Yan sanda sun kama mutane 96 da ake zargi da aikata laifuka tare da kuɓutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su a Najeriya
  • An gudanar da samamen ne a jihohi 36 da Abuja tsakanin 26 ga Satumba da 2 ga Oktoba 2026, kamar yadda sanarwa ta bayyana
  • Rundunar ta kwato bindigogi 16, harsasai 31 da motoci 16, yayin da aka kashe wasu mutane biyu da ake zargi da ɗaukar makamai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja, Najeriya — Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta kama mutane 96 tare da kuɓutar da mutane 42 da aka yi garkuwa da su a wasu ayyukan kakkabe 'yan ta'adda da ta gudanar a faɗin ƙasar.

An gudanar da ayyukan ne tsakanin 26 ga Satumba da 2 ga Oktoba 2026 a jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar, CSP Ani Ineidu, ya bayyana hakan a cikin rahoton ayyukan rundunar na mako-mako.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Sabon rikici ya barke a Neja, an samu asarar rayuka

Ya ce an kuma kwato bindigogi 16, harsasai 31 da motoci 16, yayin da aka kashe wasu mutane biyu da ake zargin na ɗauke da makamai.

Yadda aka kama 'yan ta'adda a Najeriya
'Yan sanda sun kama 'yan ta'adda 96, sun kubutar da mutum 42 | Hoto: GettyImages
Source: Getty Images

Ineidu ya ce an kama waɗanda ake zargin ne bisa laifuka da suka haɗa da garkuwa da mutane, fashi da makami, kisan kai, ’yan bindiga, ƙungiyoyin asiri, ta’addanci da satar shanu.

An ceto mutane a Sokoto

A jihar Sokoto, ’yan sanda da jami’an soji sun dakile wani harin ’yan bindiga tare da kuɓutar da mutane 30 da aka yi garkuwa da su.

Rahoton ya ce ’yan bindigan sun tare mahadar kauyen Katuru tare da kai hari kan motocin fasinjojin da ke dawowa daga kasuwar mako-mako ta kauyen Tidibale.

Jami’an tsaro sun yi musayar wuta da maharan, inda suka tilasta musu tserewa zuwa daji tare da barin waɗanda suka yi garkuwa da su.

An kuɓutar da mutane 30 ba tare da rauni ba, yayin da aka kai wasu mutum biyu da suka samu raunukan harbin bindiga asibiti.

Ayyuka a jihohi daban-daban

A Rivers, ’yan sanda sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi tare da kama wani da ake zargi. An kuma kwato bindigar AK-47, harsasai uku da babur mai ƙafa uku.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi barazanar cafke Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero a Kano

A Gombe, wani samame na haɗin gwiwa tsakanin ’yan sanda, sojoji, DSS, mafarauta da ’yan banga ya kai ga kama mutane huɗu da kuɓutar da wasu mutum biyu a gundumar Ribado ta Bajoga.

A Kogi, jami’an tsaro sun kuɓutar da wani ma’aikacin kamfanin sadarwa da aka yi garkuwa da shi a yankin Kabba.

A Delta, ’yan sanda sun kuɓutar da wata mata mai shekara 23 da aka yi garkuwa da ita domin neman N245,000 kudin fansa. An kama mutane shida a kan lamarin.

A Anambra kuma, ’yan sanda da ’yan banga sun kama mutane 13 da ake zargi da kasancewa ’yan ƙungiyar asiri tare da kwato miyagun ƙwayoyi da babura shida.

An dakile yunkurin garkuwa da mutane a Katsina

A Katsina, jami’an tsaro sun dakile wani yunƙurin garkuwa da matafiya a kan titin Funtua zuwa Zaria, kamar yadda jaridar Tribune Online ta ruwaito.

Daga bisani, jami’an sun kuɓutar da mutane huɗu da aka yi garkuwa da su waɗanda aka same su a cikin wata mota.

A wani samame daban, ’yan sanda sun kwato abubuwan fashewa 159 da ake zargin za a iya amfani da su wajen ƙera bama-bamai. An gano su ne a cikin wata Toyota bas da ke tafiya daga Kano zuwa Kongolam a Jamhuriyar Nijar.

Kara karanta wannan

An yi jina jina da sojoji suka gwabza fada da 'yan ta'adda, an rasa rayuka

Yadda ta kaya a jihar Benue

A Benue, ’yan sanda sun kama wani da ake zargi da kasancewa ɗan ƙungiyar asiri tare da kwato bindigogi da harsasai.

Ineidu ya ce duk waɗanda aka kama suna hannun jami’an tsaro yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike da ƙoƙarin kamo sauran waɗanda suka tsere.

Ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da amfani da bayanan sirri da haɗin gwiwa da al’umma da sauran hukumomin tsaro wajen yaƙi da miyagun laifuka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and leads the Hausa Desk at Legit.ng. He is AfricaCheck's ambassador and HumAngle Technology and Civic Impact Fellow. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. His commitment to excellence has earned him recognition, including the Legit Fearless Team Player of the Year 2023 and 2024 Distinguished Editorial Leadership Award. Email: salisu.ibrahim@corp.legit.ng