Ana cikin Jimamin Hatsarin Jirgi, An Shiga Sansanin Sojojin Najeriya An Kashe Sama da 10
- Akalla sojoji 12 da fararen hula biyar ne aka kashe da ’yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji a ƙauyen Bindin a ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara
- ’Yan bindigar sun kai harin ne da babura da dama, inda suka yi musayar wuta da sojoji na tsawon sa’o’i
- Rahotanni sun ce harin ramuwar gayya ne bayan an kashe wani ɗan bindiga da ya yi yunkurin kai hari kan masu haƙar ma’adanai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Akalla sojoji 12 da fararen hula biyar ne aka kashe, yayin da ’yan bindiga sun kai hari wani sansanin sojoji a ƙauyen Bindin, ƙaramar hukumar Maru ta jihar Zamfara.
Baya ga kashe rayuka 17 a harin, an ce maharan sun kuma yi awon gaba da wasu mutane biyu zuwa maboyarsu da ba a san inda take ba.

Source: Twitter
Wani mazaunin yankin, Mukhtar Bello, ya shaida wa Leadership cewa harin ya faru ne ranar Talata, lokacin da ’yan bindiga suka kutsa wurin da sojojin suke a kan babura, sannan suka bude musu wuta.
Ya ce harin ramuwar gayya ne bayan an kashe wani ɗan bindiga da ya yi yunkurin kai hari kan masu haƙar ma’adanai ranar Litinin, amma aka yi galaba a kansa tare da kwace bindigarsa kirar AK-47.
Majiyar ta ce shahararren shugaban dabar ’yan bindiga, Gwaska Dankarami, ne ya jagoranci harin.
An shafe sa’o’i ana musayar wuta
A cewar majiyar, sojoji sun yi artabu mai tsanani da ’yan bindigar na tsawon sa’o’i, amma daga bisani suka sha kashi saboda yawan ’yan bindigar da suka kai harin.
Ya ce an kashe sojoji 12 a arangamar, yayin da aka sace wasu biyu, sannan maharan suka kwashe makamai da sauran kayan aikin sojoji.
Ƙoƙarin jin ta bakin Rundunar Sojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Fansan Yamma a Gusau bai yi nasara ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.
NDC ta yi Allah wadai da harin
A halin da ake ciki, jam’iyyar NDC ta jihar Zamfara ta yi Allah wadai da harin, tana mai bayyana shi a matsayin kisan kiyashi.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar, Murtala Gusau, ya sanya wa hannu, NDC ƙarƙashin jagorancin Alhaji Surajo Garba Maikatako ta jajanta wa al’ummar Bindin kan asarar rayukan da aka yi.

Source: Facebook
Sai dai jam’iyyar ta nuna damuwa kan zargin rashin kasancewar Gwamna Dauda Lawal a jihar a lokacin da lamarin ya faru.
NDC ta ce gwamnan yana cikin tawagar gwamnatin tarayya da ta halarci taron musayar ra’ayi tsakanin shugabannin Najeriya da Habasha kan manufofin abinci mai gina jiki a Addis Ababa lokacin da harin ya faru.
Dakarun sojoji sun dakile harin ISWAP
Kun ji cewa Dakarun Bataliya ta 101 ta Sojojin Najeriya da ke Kukawa, Jihar Borno, sun yi nasarar dakile wani babban hari da ’yan ta’addan ISWAP suka kai sansaninsu.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun ce ’yan ta’addan sun kai harin ne daga wurare huɗu daban-daban, a wani yunƙuri na mamaye sansanin sojojin.
Majiyoyin tsaro sun ce dakarun sojojin sun samu nasarar hallaka yan ta'adda akalla 25 yayin da sauran suka gudu dauke da raunuka.
Asali: Legit.ng


