Trump Ya Saka Ranar da za a Bindige Tsohon Sojan Amurka, Nidal Hasan
- An sanya ranar 3 ga Disamba 2026 domin aiwatar da hukuncin kisa kan tsohon sojan Amurka Nidal Hasan, wanda ya kashe mutane 13 a harin Fort Hood a 2009
- Za a kashe Hasan ne ta hanyar harbe shi da bindigar sojoji a sansanin Fort Hood da ke Texas, inda ya kai harin, a wani hukuncin da zai zama na farko tun 1961
- Harin na 2009 ya yi sanadin mutuwar mutane 13 tare da jikkata wasu 32, yayin da iyalan waɗanda suka mutu aka sanar da ranar da aka tsara aiwatar da hukuncin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Washington – An sanya ranar 3 ga Disamba 2026 domin aiwatar da hukuncin kisa kan tsohon babban jami’in Sojan Amurka, Nidal Malik Hasan, wanda ya kashe mutum 13 a wani harbi da ya kai sansanin Fort Hood da ke Texas a 2009.
Hasan zai fuskanci hukuncin kisa ne ta hanyar harbe shi da bindigar sojoji a sansanin da ya kai harin, lamarin da zai zama hukuncin kisa na farko da sojojin Amurka suka aiwatar cikin shekaru 65.

Source: Getty Images
Gwamnatin Amurka ta tabbatar da ranar kashe tsohon sojan a wani sako da ta wallafa a shafinta na X da yammacin ranar Talata.
Trump ya ce a kashe Hasan
Mai magana da yawun Pentagon, Sean Parnell, ya bayyana cewa Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth, ne ya bayar da shawarar a yi wa Hasan kisan gilla ta hanyar harbe shi da bindigar sojoji.
Rahotanni sun ce ranar da aka tsara za a aiwatar da hukuncin ita ce 3 ga Disamba, 2026 kuma za a yi hakan a Fort Hood, inda Hasan ya kai harin shekaru 17 da suka gabata.
Yadda Hasan ya kai harin
A ranar 5 ga Nuwamba 2009, Hasan, wanda a lokacin likitan kwakwalwa ne a rundunar sojin Amurka, ya buɗe wuta kan sojoji da ke cibiyar shirye-shiryen tura sojoji aiki.
Harin ya kashe mutane 13 tare da jikkata wasu 32. Hasan ya harba harsasai sau 146 kafin jami’an tsaro su mayar da martani, inda aka harbe shi kuma ya samu nakasa daga ƙirji zuwa ƙasa.
An yanke masa hukuncin kisa ne a shekarar 2013 bayan wata kotun soji ta same shi da laifin kisan mutane 13 da kuma yunƙurin kashe wasu 32. Tun daga lokacin yake tsare a sashen masu jiran hukuncin kisa na Fort Leavenworth da ke Kansas.

Source: Getty Images
Me ya sa aka zaɓi harbe shi?
CBS ta wallafa cewa dokokin Sojojin Amurka sun tanadi cewa shugaban ƙasa ne kaɗai ke da ikon amincewa da hukuncin kisa na soja.
Gyaran dokar da aka yi a 2019 ya cire ambaton allurar guba a matsayin hanyar aiwatar da hukuncin, tare da barin hanyar kisan ga shawarar Shugaban Sojojin Amurka bisa tsarin da aka tanada.
Idan aka sanar da fursunan cewa shugaban ƙasa ya amince da hukuncin, kwamandan gidan yarin ne ke sanar da shi da kansa tare da limamin sojoji da kuma lauya idan akwai.
Maganar zanga-zanga a Faransa
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya danganta zanga-zangar ɗalibai da ta barke a Faransa da matsalar yawan bakin haure da kuma Musulunci.
Trump ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa, inda ya ce abin da ke faruwa a Faransa ya samo asali ne daga “yawan hijira da ya wuce kima”.
Ya kuma yi zargin cewa zanga-zangar ba ta da alaƙa da makarantu, yana mai cewa Musulunci na son “ƙwace” Faransa, yayin da rahotanni suka nuna cewa ɗaliban sun gudanar da zanga-zangar ne kan yanayin makarantu.
Asali: Legit.ng

