
Cikakken Bincike







A karon farko, kasar Indiya ta yi nasarar saukar da kumbonta a kusurwar Kudu ta duniyar wata bayan kumbon Rasha ya tarwatse a kokarin cilla shi duniyar wata.

Binciken kwakwaf ya bayyana gaskiyar wani faifan bidiyo inda aka gano Janar Tchiani na cewa ba zai saurari Shugaba Tinubu ba saboda gwamnatinsa Haramtacciya ce.

Wasu 'yan bindiga sun hallaka wani tsohon dan sanda Mista Sampson Owobo da mai dakinsa a Owerri ta jihar Imo, ya kasance tsohon mataimakin sifetan 'yan sanda.

Kotun majistare da ke Kado a birnin Abuja ta daure ma'aikacin JAMB, Emmanuel Odey kan satar kwamfuta da ta kai Naira dubu 350 don biyan kudin haya na gidansa.

'Yan sanda sun gurfanar da wata mata a gaban kotu, Blessing Udoh kan zargin ba wa hukumar bayanan karya kan cewa an yi kisan kai a jihar Legas, kotu ta daure ta

Daya daga cikin 'yan uwan marigayi Shekh Ibrahim Albanin Kuri, Dahiru Halliru ya bayyana halin da iyalansa ke ciki a yanzu bayan mutuwar malamin a jihar Gombe.

Wasu matasa matsafa sun yi ajalin wani Fasto mai suna Dada Itopa a cikin gonarsa bayan sun yi basaja cewa su leburori ne a jihar Ondo, sun sari matarsa da adda.

Kotun da ke zamanta a birnin Abuja da gurfanar da wani sanannen Fasto mai suna Uche Aigbe kan zargin mallakar bindiga kirar AK-47 a cikin majami'arsa a Abuja.

Gwamnatin jihar Ekiti ta dakatar da wani babban basarake mai suna Cif Gabriel Bodunde kan rashin biyayya da kuma wuce gona da iri kan matakin doka a jihar.
Cikakken Bincike
Samu kari