INEC Ta Yi Magana kan Hukuncin Kotun da Zai Iya Shafar Takarar Su Pantami
- INEC ta fara nazarin hukuncin Kotun Ƙoli kan tanade-tanaden Dokar Zaɓe da suka shafi cancantar wasu ’yan takara shiga zaɓen fitar da gwani
- Hukuncin ya haifar da tambayoyi kan ’yan siyasar da suka koma sababbin jam’iyyu bayan sun kasa samun tikitin jam’iyyunsu na farko
- Shugaban INEC, Joash Amupitan, ya ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe daga jam’iyyu, ’yan takara da majalisar tarayya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta fara nazarin hukuncin Kotun Ƙoli kan wasu tanade-tanaden Dokar Zaɓe ta 2026 da ka iya shafar cancantar wasu ’yan takara a zaɓen 2027.
Kotun Ƙolin ta tabbatar da ingancin Sashe na 77 da 84 na Dokar Zaɓe ta 2026, bayan kararrakin da Zenith Labour Party (ZLP) da Social Democratic Party (SDP) suka shigar.

Source: Facebook
Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata, 6 ga watan Oktoban 2026, ya bayyana cewa sun fara nazari kan hukuncin, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Hukuncin ya haifar da tambayoyi kan wasu ’yan takara
Tun bayan hukuncin, an samu ra’ayoyi daban-daban kan abin da hukuncin zai haifar ga ’yan siyasar da suka koma wasu jam’iyyu bayan sun kasa samun tikitin jam’iyyun da suke ciki tun farko.
A Gombe, an fara nuna damuwa kan makomar Farfesa Isa Ali Pantami sakamakon lokacin da ya sauya sheka daga All Progressives Congress (APC) zuwa Peoples Democratic Party (PDP).
A jihar Neja kuma, an sake samun tambayoyi kan makomar Muhammad Nami, ɗan takarar PDP na gwamnan jihar a zaɓen 2027.
Hukuncin ya kuma haifar da ra’ayoyi daban-daban kan cancantar tsohon Sufeto-Janar na ’yan sanda, Mohammed Abubakar Adamu, a jihar Nasarawa.
Tsohon IGP ɗin ya maye gurbin Adamu Angba, wanda shi ne ɗan takarar SDP na gwamnan Nasarawa, bayan Angba ya janye daga takarar.
Amupitan ya ce INEC ta samu ƙorafe-ƙorafe
Sai dai da yake magana a wani taron manema labaran, Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ta samu ƙorafe-ƙorafe daga jam’iyyun siyasa, ’yan takara da ba su gamsu da matakan da aka ɗauka ba, da kuma mambobin majalisar tarayya.
Amupitan ya ce INEC ta karɓi kwafin hukuncin Kotun Ƙoli da aka tabbatar da sahihancinsa, wato Certified True Copy (CTC), a ranar Talata, kuma tana nazarinsa kafin ta yanke shawarar matakin da ya dace.
INEC na nazarin hukuncin
Ya ce hukumar INEC ta samu korafe-korafen da ke neman a duba yadda hukuncin zai shafi aiwatar da Sashe na 77 na Dokar Zaɓe da kuma jadawalin ayyukan zaɓen 2027.
“Mun samu ƙorafe-ƙorafe daga wasu jam’iyyun siyasa, ’yan takara da suka nuna rashin gamsuwa, har ma da majalisar tarayya, dangane da hukuncin Kotun Ƙoli na baya-bayan nan kan INEC da Zenith Labour Party, wanda aka yanke ranar 24 ga Satumba, 2026."
“Hukuncin ya tabbatar da cewa Sashe na 77, ƙananan sassa na 5 zuwa 7 na Dokar Zaɓe ta 2026 sun yi daidai da kundin tsarin mulki, sannan ya kuma tabbatar da sabon jadawalin ayyukan INEC na zaɓen 2027."
“Mun karɓi kwafin hukuncin da aka tabbatar da sahihancinsa ne a safiyar yau, kuma ana nazarinsa,” in ji Amupitan.
Sunayen ’yan takara da ke cikin ce-ce-ku-ce
Daga cikin ’yan takarar da batun cancantarsu ya jawo hankali akwai Kingsley Chinda, ɗan takarar APC na gwamnan jihar Rivers.
Haka kuma akwai Ovie Omo-Agege, ɗan takarar Nigeria Democratic Congress (NDC) na kujerar Sanatan Delta ta Tsakiya.
Sauran sun haɗa da tsohon gwamnan Cross River kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na Peoples Redemption Party (PRP), Donald Duke, da tsohon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, Victor Ochei.
Ana jiran matakin da s za ta ɗauka
Ana sa ran nazarin da INEC ke yi zai fayyace yadda hukuncin Kotun Ƙoli zai shafi ’yan takarar da lamarin ya shafa, jam’iyyun siyasa da kuma shirye-shiryen hukumar na gudanar da zaɓen 2027.
Sai dai a halin yanzu, INEC ba ta bayyana cewa ta soke ko ta tabbatar da cancantar wani daga cikin ’yan takarar da ake magana a kansu ba, yayin da nazarin hukuncin ke ci gaba.

Kara karanta wannan
An sanya sabon lokacin yanke hukunci a shari'ar sojojin da suka yi yunkurin kifar sa Tinubu

Source: Facebook
Gargadin INEC ga 'yan siyasa
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar INEC ta gargadi ’yan siyasa da su guji duk wani mataki da zai iya jefa rayukan ’yan Najeriya cikin hadari yayin shirye-shiryen babban zaben 2027.
Farfesa Joasha Amupitan ya ce hukumar ba za ta bari gasar siyasa ta rikide zuwa tashin hankali, tsoratarwa ko yada kalaman da za su haddasa kiyayya ba.
Asali: Legit.ng


