Kotun Daukaka Kara Ta Shirya Yanke Hukunci a Bukatar da El Rufai Ya Dade Yana Nema
- Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Kaduna ta saurari ƙarar Nasir El-Rufai kan ƙin amincewa da belinsa da babbar kotu ta yi
- Lauyan ICPC ya nemi kotun ta yi watsi da ƙarar, yana cewa an riga an ƙi amincewa da buƙatun belin El-Rufai har sau uku
- Lauyan El-Rufai ya nemi a ba tsohon gwamnan beli, yana cewa laifuffukan da ake tuhumarsa da su ba wadanda za a ki amincewa da bukatarsa ba ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kaduna - Kotun daukaka kara da ke Kaduna ta tanadi hukunci kan ƙarar da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shigar.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya shigar da karar ne yana ƙalubalantar ƙin amincewa da buƙatar belinsa.

Source: Facebook
Mai shari’a Onyekachi Aja Otisi ne ya jagoranci zaman kotun, inda aka saurari hujjojin lauyoyin Hukumar ICPC da kuma na El-Rufai, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Bayan sauraron bangarorin biyu, kotun ta tanadi hukunci, amma ba ta sanya ranar da za ta yanke hukuncin ba.
ICPC ta nemi a yi watsi da ƙarar
Lauyan ICPC, Ayodeji Adedipe, ya buƙaci kotun ta yi watsi da ƙarar, yana mai cewa babbar kotu jihar Kaduna ta yi daidai da ta ƙi amincewa da belin tsohon gwamnan.
Adedipe ya ce El-Rufai ya shigar da buƙatun beli daban-daban guda uku a gaban kotun da ke sauraron shari’ar, amma an ƙi amincewa da dukkaninsu.
A cewarsa, an yi watsi da buƙatar farko, yayin da aka ƙi ta biyu bayan El-Rufai ya kasa gabatar da wasu kebabbun dalilai da za su ba shi damar sake neman beli.
Ya ce daga baya an shigar da buƙatar beli ta uku, wadda ita ma aka ƙi amincewa da ita, amma El-Rufai ya zaɓi ya ɗaukaka ƙarar hukuncin da aka yanke kan buƙatar belin ta biyu.
ICPC ta ce an ɓoye bayanin buƙatar beli ta uku
Lauyan ICPC ya yi zargin cewa El-Rufai bai bayyana wa Kotun Ɗaukaka Ƙara cewa an kuma ƙi amincewa da buƙatar belin ta uku ba.
Saboda haka, Adedipe ya ce ƙarar ba ta da ingantaccen dalili, don haka ya nemi kotun ta yi watsi da ita.
Lauyan El-Rufai ya nemi a ba shi beli
Sai dai lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, SAN, ya roƙi kotun da ta soke hukuncin ƙaramar kotun tare da bayar da belin tsohon gwamnan har zuwa lokacin da za a kammala shari’ar.
Erokoro ya yi hujjar cewa laifufdukan da ake tuhumar El-Rufai da su ba laifuffukan kisa ba ne, don haka babu dalilin da zai sa a hana shi beli.
Ya ce beli haƙƙi ne da kundin tsarin mulki ya tanada, sai dai a wasu laifuffuka na musamman, yana mai cewa ci gaba da tsare wanda yake karewa a hannun ICPC na kawo cikas ga shirye-shiryen kare kansa.
Bayan sauraron hujjojin bangarorin biyu, kotun daukaka kara ta tanadi hukuncin ƙarar, amma ba ta sanya ranar da za ta yanke hukuncin ba.

Source: Original
Buba Galadima ya soki Tinubu kan El-Rufai
A wani labarin kuma, kun ji cewa Buba Galadima, ya zargi Shugaba Bola Tinubu da wasu na kusa da shi da rashin nuna godiya ga tsohon Gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai.
Galadima ya ce El-Rufai ya taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa Tinubu samun nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Asali: Legit.ng


