Yana Hanyar zuwa Jana'izar Mahaifinsa, Ƴan Bindiga Sun Harbe Matashi a Sokoto
- ‘Yan bindiga sun bude wuta kan wata mota a hanyar Shinkafi zuwa Isa, inda suka harbe wani matashi kusa da Gadilar Sule Ishsha
- Matashin yana tafiya ne daga Abuja zuwa jana’izar mahaifinsa lokacin da ‘yan bindigar suka kai masa hari, kasa da kilomita biyu da garin Isa
- Lamarin ya jefa jama’a cikin jimami, yayin da ake sake tambayar tsawon lokacin da za a ci gaba da barazanar rayukan matafiya a hanyoyin Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Sokoto - Yan bindiga na ci gaba da cin karensu babu babbaka musamman a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.
Miyagun sun bude wuta kan wata mota a hanyar Shinkafi zuwa Isa, inda suka harbe Jamilu Isah Modawa kusa da Gadilar Sule Ishsha.

Source: Twitter
Majiyar tsaro daga Bakatsine ta tabbatar da cewa lamarin ya faru ne kasa da kilomita biyu da garin Isa a jihar Sokoto.
An kama jami'in tsaro da taimakawa yan bindiga
Rashin tsaro ya yi kamari a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya wanda ya jawo asarar rayuka da dukiyoyin al'umma.
Al'umma da dama na ta kira ga hukumomi da su dauki matakan gaggawa domin dakile ayyukan ta'addanci a yankin.
Sai dai hakan na ci gaba da samun tsaiko saboda yadda wasu daga cikin mutane ke ci gaba da ba yan bindiga taimako, duba da yadda ake yawan kama matasa kan wannan zargi.
Jami’an tsaro sun kama wani sabon ɗan koyon aikin tsaron daji, Zahraddin Abdullahi Karadua, bisa zargin kai wa ’yan bindiga alburusai a Matazu, Katsina.
A wani bidiyo, Zahraddin ya bayyana cewa wani mutum mai suna Muhammadu ya ba shi alburusai a Kano, ya kai su Karadua, sannan ya miƙa wa Sahiba.
Sahiba ta amsa karɓar alburusai, inda ake zargin ta kai su wani sansanin ’yan bindiga da ake zargin yana kusa da ƙauyen Maharba.
Yadda aka bindige matashi a jihar Sokoto
Matashin da aka harbe yana tafiya ne daga Abuja zuwa halartar jana’izar mahaifinsa, abin da ya dugunzuma yan uwansa da abokan arziki.
Hakan ya kara tsunduma mutane cikin fargaba duba da cewa ya faru ne lokacin da yake cikin jimamin rasuwar mahaifinsa.
Lamarin abin takaici ne matuka, yayin da ake ci gaba da tambayar yawan rayukan da za su kasance cikin hadari a kan hanyoyin Najeriya kafin a kawo karshen wannan matsalar tsaro.
Yan bindiga sun sace manoma 50
A wani labarin, an ji cewa ana zargin ’yan bindiga da sace manoma da wasu ma’aikatan gona a Mariga, yayin da shugaban ƙaramar hukumar ya ce adadin waɗanda aka sace ya kai 47.
Shugaban ƙaramar hukumar ya ce masu garkuwa sun tuntubi wasu ’yan uwan waɗanda aka sace, inda suka nemi N2m a matsayin kuɗin fansa kan kowane mutum.
Yan sandan Niger sun tabbatar da sace sama da mutane 20 a yankin, lamarin da ya haifar da bambanci kan adadin waɗanda aka yi garkuwa da su.
Asali: Legit.ng

