Minista Ya Fasa Kwai, An Ji Yadda Ake Shirin Karawa Atiku 'Hawan Jini' kafin Zaben 2027

Minista Ya Fasa Kwai, An Ji Yadda Ake Shirin Karawa Atiku 'Hawan Jini' kafin Zaben 2027

  • Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya bayyana burinsa na kara wa Atiku Abubakar da yan adawa hawan jini a fagen siyasa kafin 2027
  • Wike ya yi ikirarin cewa sauye-sauyen siyasa da ke faruwa za su haifar da babbar ƙawancen Rainbow Coalition na goyon bayan Tinubu
  • Ministan ya yi watsi da ikirarin cewa nasarar Gwamna Ademola Adeleke na jihar Osun ta ƙara wa ’yan adawa ƙarfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce manufarsa kafin zaɓen 2027 ita ce tabbatar da ’yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar da Peter Obi, ba su samu kwanciyar hankali ba ta hanyar ƙara musu hawan jini.

Wike ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai ranar Juma’a a Abuja, bayan duba wasu ayyukan raya birnin da ake gudanarwa a Babban Birnin Tarayya (FCT).

Kara karanta wannan

ADC ta fito da bayani, an ji dalilin Atiku na ƙin sa hannu a yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2027

Wike.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike
Source: Facebook

Tsohon gwamnan na jihar Ribas ya kuma dage cewa a halin yanzu babu wata jam’iyyar adawa da za a iya cewa ita ce ke kan gaba, kamar yaddajaridar Vanguard ta ruwaito.

Wike ya kuma yi watsi da ra’ayin cewa sake zaɓen gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya ƙara wa ’yan adawa ƙarfi.

Wike ya yi magana kan Adeleke

Da yake magana kan ziyarar da Adeleke ya kai wa Shugaba Bola Tinubu da shi, Wike ya ce sauye-sauyen siyasa da yake sa ran za su faru cikin makonni masu zuwa za su kafa ƙawancen Rainbow Coalition domin goyon bayan Tinubu.

Ya ce Adeleke ɗan jam’iyyar PDP ne, amma rikicin cikin gida da ya dabaibaye jam’iyyar ya sa ya nemi wata kafa da zai tsaya takara a karo na biyu, inda ya samu tikitin Accord.

Wike ya ce abin da ya faru a daren Alhamis wani taro ne na duba ƙawancen Rainbow Coalition, yana mai cewa Adeleke na goyon bayan Tinubu duk da cewa ya tsaya takara ne a ƙarƙashin wata jam’iyya.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Davido ya je har gidan Wike ya ce sun kifar da APC

Ya ƙara da cewa a makonni masu zuwa za a ga ƙarin sauye-sauyen siyasa da za su ƙarfafa ƙawancen masu goyon bayan Tinubu.

Wike na kokrin karawa Atiku hawan jini

Wike ya yi watsi da ikirarin wasu ’yan jam’iyyar ADC cewa sun taimaka wajen samun nasarar Adeleke a zaɓen Osun.

Da aka tambaye shi ko yana damuwa da yadda shugabannin adawa, musamman Atiku da Obi, ke kallon alakar da yake ƙulla wa Adeleke, Wike ya ce ba ruwansa da yadda suke ji.

Peter Obi da Atiku.
Manyan yan takarar shugaban kasa na tsagin adawa, Peter Obi da Atiku Abubakar Hoto: Peter Obi, @Atiku/X
Source: Facebook

Wike ya bayyana cewa ba aikinsa ba ne ya tabbatar da cewa ’yan adawa sun ji daɗin yanayin siyasar da ake ciki, domin burinsa shi ne ganin tawagarsa ta samu nasara.

“Ba na son su ji daɗi. Aikina shi ne in tabbatar ba su ji daɗi ba a kullum, saboda za su riƙa samun hawan jini,” in ji shi.

Wike ya hango nasarar Tinubu a 2027

Kun ji cewa Ministan Abuja, Niyesom Wike ya ce Shugaba Bola Tinubu zai samu saukin lashe zaben shugaban kasa na 2027 fiye da na shekarar 2023.

Ya ce rarrabuwar kawunan jam’iyyun adawa za ta sanya su gaza wajen hada karfi da kalubalantar Tinubu a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262