Tsohuwar Matar Yaron El Rufai Ta Yi Magana Shekaru 3 da Mutuwar Aurensu

Tsohuwar Matar Yaron El Rufai Ta Yi Magana Shekaru 3 da Mutuwar Aurensu

  • Halima Nwakaego Kazaure ta bar gidan Bashir El-Rufai tunda aurensu ya zo karshe a tsakiyar 2024
  • Yanzu ‘yar kasuwa kuma lauyar ta kan yi magana wajen abin da ya shafi mata masu tarbiyyar yara
  • Baya ga kula da tagwayen da suka haifa, ta bude gangariyan wuri da ake saida abinci a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - ‎Barista Halima Nwakaego Kazaure ta fito bainar jama’a ta yi magana game da halin da ta ke ciki yau a rayuwa.

‎Halima Nwakaego Kazaure ta yi tsokaci ne a kan harkar tarbiyyar yara, kasuwanci da soyayya bayan mutuwar aurenta.

Halima Kazaure da Bashir El-Rufai
Lokacin auren Halima Kazaure da Bashir El-Rufai a 2020 da kuma hoton murnar zamanta lauya a 2019 Hoto: @Fashinseriesng (Instagram)/limakazaure (x)
Source: UGC

Wani hali Halima Kazaure take ciki yanzu?

A wani rubutu da ta yi a shafinta na Memoirs, ta tabbatar da cewa ta rabu da mutumin da ta aura a watan Nuwamban 2020.

Dama can kwanakin baya an ji Bashir El-Rufai yana yaba yawun wata a dandalin X, a karshe ya tabbatar da shi tazuru ne.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya ta yi magana kan sayar da litar fetur a N200

Rubutun da ta wallafa a ranar 18 ga Agustan 2026 ya bayyana cewa auren ya mutu tun a cikin watan Yulin shekarar 2024.

‘Yar kasuwar ta nuna ta bar gidan auren nata ne a lokacin 'ya ‘yan da ta samu da Bashir El-Rufai suna shekaru biyu da haihuwa.

A halin yanzu ‎Halima Nwakaego Kazaure ta dukufa wajen tarbiyyar yara, harkar kasuwancinta da kula da cutar ADHD.

Baya ga haka. Legit Hausa ta fahimci tana da wurin saida abinci da kayan kwadayi a Abuja.

Mahaifin Halima Nwakaego Kazaure mutumin Jigawa ne, uwar kuma daga kasar Ibo a yankin Kudu maso gabashin Najeriya.

Halima Kazaure ta sake jarraba soyayya?

Ta ce watanni bayan mutuwar aurenta, ta hadu da wani mutumin, amma shi ma suka rabu kafin a je ko ina.

A shafin na Substack ta ke cewa masu iya magana na cewa maza za su lalata wa mutum rayuwa.

Halima ta ce dama tun farko ba ta wani yi amanna da aure ba kuma tun kafin a kai ta daki, ta san cewa nata ba zai kai labari ba.

Kara karanta wannan

FEC: Gwamnatin Tinubu ta amince a kashe N438bn wajen yin tituna a Najeriya

Rahoton Premium Times ya ce wannan baiwar Allah ta ce ‘ya ‘yanta su ne kurum abin da ba ta gajiya da su a rayuwar duniyar nan.

Kasuwanci kuma ta shiga wannan da wancan, kuma ta rasa wasu daga cikin na kusa da ita a cikin ‘yan shekarun baya-bayan nan.

A cewarta, tamkar ta shiga gidan auren da ake shirya jana’izarsa ne.

Daga labarin da Leadership ta fitar, ba mu ji inda ta kira sunan tsohon mai gidanta ko surukanta, iyalin tsohon gwamnan Kaduna ba.

Duk da yadda maza su ka yi mata butu-butu, ba ta cire rai ba, tana rayuwa da shakkun maza da kuma tsananin amanna da soyayya.

Ga wanda ba ta yarda da maza sosai ba, ta ce tana kuma da ‘dan karen imani da soyayya.

Auren Bashir El-Rufai da Halima Kazaure

A karshen shekarar 2020 ne aka ji gwamnan Kaduna a lokacin ya hada zuri’a da tsohon sanatan jihar Jigawa, Ibrahim Kazaure.

Diyar Ibrahim Kazaure wanda a lokacin ba ta dade da zama lauya ba, ta auri Bashir El-Rufai a babban birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan

NDC: Jam'iyyar su Kwankwaso ta zo da salo bayan INEC ta amince a fara kamfen

Idan za a iya tuna wa shekara guda bayan yin auren ne aka yi farin cikin samun tagwaye da a kan gani a shafin sada zumunta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng