An Yi wa Kabiru Gombe Babban Rashi, Bala Lau da Pantami Sun Yi Ta'aziyya

An Yi wa Kabiru Gombe Babban Rashi, Bala Lau da Pantami Sun Yi Ta'aziyya

  • Babban Sakataren JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe, ya sanar da rasuwar ɗan uwansa, Malam Abdullahi, wanda aka fi sani da Kawu Babangida
  • An sanar da cewa za a gudanar da Sallar Jana'izarsa a Masallacin JIBWIS da ke Bolari, Gombe, da misalin ƙarfe 11:00 na safe ranar Asabar, Insha Allah
  • Shugaban JIBWIS, Sheikh Abdullahi Bala Lau, da sauran malaman addini sun mika sakon ta'aziyya ga Sheikh Kabir Gombe da iyalan marigayin, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe – Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah (JIBWIS) ta sanar da rasuwar Malam Abdullahi, Kawu Babangida, wanda shi ne kanin mahaifiyar Babban Sakataren JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe.

Kara karanta wannan

Bayan nasarar Isa Ali Pantami, PDP ta kori manyan masu masa adawa 2 a Gombe

Sheikh Kabir Gombe ya gayyaci al'ummar Musulmi mazauna Gombe da kewaye zuwa halartar Sallar Jana'izar marigayin da za a gudanar a Masallacin JIBWIS da ke Bolari.

Kabiru Gombe da dan uwan shi
Sheikh Kabiru Gombe a hagu da Dan uwan shi a dama. Hoto: Muhammad Kabir Haruna Gombe
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai game da rasuwar marigayin ne a wani sako da Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe ya wallafa a Facebook.

Rahotanni sun nuna cewa za a yi wa marigayin sallah ne a yau Asabar da misalin karfe 11:00 na safe a masallacin Filin Kwallon Bolari da ke Gombe.

JIBWIS ta yi ta'aziyya

Shugaban JIBWIS na Ƙasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin da 'yan uwansa da kuma al'ummar Kuri da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba ta Jihar Gombe.

Sheikh Bala Lau ya kuma mika ta'aziyya ta musamman ga Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe da sauran 'yan uwa da abokan arzikin marigayin bisa wannan babban rashi.

Izala ta wallafa a Facebook cewa ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai kyawawan halaye da kyautata mu'amala da zumunci, tare da roƙon Allah Ya gafarta masa kura-kuransa kuma Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware gwamnonin Arewa 3, za ta karrama su saboda kokarinsu

Taswirar jihar Gombe
Taswirar jihar Gombe a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

Sheikh Pantami ya yi ta'aziyya

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙin Zamani, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami, shi ma ya mika ta'aziyyarsa ga Sheikh Muhammad Kabir Haruna Gombe bisa rasuwar ƙanin mahaifiyarsa.

Sheikh Pantami ya ce ya miƙa ta'aziyya ga iyalan marigayin, 'yan uwansa, abokansa da sauran masoyansa bisa wannan babban rashi.

A sakon da ya wallafa a Facebook, ya roƙi Allah Ya gafarta wa marigayin, Ya yi masa rahama, kuma Ya sanya Aljanna ce makomarsa tare da sauran iyaye, malamai, 'yan uwa da masoyansa.

Matar sarki a Gombe ya rasu

A wani labarin, mun ruwaito rasuwar Hajiya Amina Saleh Muhammad, matar Mai Kaltungo kuma Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Gombe, Saleh Muhammad Umar, OON.

Rasuwar Hajiya Amina ta jawo jimami ga iyalan gidan sarautar Kaltungo da al'ummar yankin, inda aka mika sakon ta'aziyya ga Mai Kaltungo da sauran 'yan uwa da abokan arziki.

Jama'a sun roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya bai wa Mai Kaltungo da iyalansa ƙarfin zuciya da haƙurin jure wannan babban rashi, tare da ci gaba da kare masarautar Kaltungo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng