Kwana Ya Kare: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub Ya Rasu

Kwana Ya Kare: Babban Malamin Addinin Musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub Ya Rasu

  • An tabbatar da rauwar daya daga cikin sanannun malaman addinin musulunci a jihar Kogi da ke Arewacin Najeriya, Malam Jamiu Yaakub
  • Iyalin Malam Jamiu Yaakub sun sanar da rasuwarsa, inda suka bayyana shi a matsayin mutum mai kyawawan halaye da gaskiya
  • Yaakub ya kasance Shugaban NASFAT na Abobo kuma ya shafe tsawon rayuwarsa yana koyarwa da renon dalibai

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abobo, Jihar Kogi - An tabbatar da rasuwar Sheikh Jamiu Yaakub, malamin addinin Musulunci kuma malamin makaranta da ya yi ritaya.

Legit.ng ta samu labarin cewa Yaakub, Naibin Limamin Babban Masallacin Abobo da ke Jihar Kogi, ya rasu ne a daren Laraba, 30 ga watan Satumba, 2026.

Malam Jamiu Yaakub
Babban malamin addinin musulunci a jihar Kogi, Malam Jamiu Yaakub Hoto
Source: Facebook

Iyalan marigayin sun sanar da rasuwarsa a wata sanarwa da suka wallafa a shafin Facebook ranar Juma’a, 2 ga watan Oktoba, 2026.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: An buɗe wa Tinubu ƙofar da zai iya raba Atiku da mataimakinsa kafin zaɓen 2027

A cikin sanarwa da iyalinsa suka fitar, sun bayyana cewa za a rika tunawa da Yaakub a matsayin mutum mai kyawawan halaye.

An kuma yaba masa kan jajircewarsa wajen tabbatar da adalci, tawali’u da gaskiya a tsawon rayuwarsa.

An tuna da shugabancin malamin

Sheikh Yaakub ya shafe wani kaso mai tsoka na rayuwarsa yana koyarwa a aji, inda ya taimaka wajen gina rayuwar dalibai kafin ya yi ritaya daga koyarwa.

Bayan aikinsa na koyarwa, ya kuma taka muhimmiyar rawa a matsayin jagoran al’umma, inda ya bayar da gudunmawa wajen ci gaban Musulunci tare da karfafa hadin kai tsakanin mutanen da ke kewaye da shi.

Marigayin ya kasance Shugaban kungiyar NASFAT na Abobo, matsayin da iyalinsa suka ce ya rike shi cikin gaskiya, jajircewa da kishin aiki.

NASFAT ta taimaka wajen jana’iza

Iyalin sun yi amfani da sanarwar wajen nuna godiyarsu kan dimbin goyon bayan da aka ba su yayin shirye-shiryen jana’izar.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Sun yaba wa NASFAT Kogi Central, musamman reshen Abobo, da sauran kungiyoyin NASFAT daga kananan hukumomi daban-daban saboda yadda suka taimaka wajen tsara al’amuran jana’izar da tallafa musu a wannan lokaci.

Iyalin sun kuma gode wa abokai, malaman addini da masu fatan alheri da suka yi tafiya daga sassa daban-daban na kasar domin halartar jana’izar tare da jajantawa iyalan marigayin.

Jihar Kogi.
Taswirar jihar Kogi da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A karshen sanarwar, iyalan sun roki Allah ya gafarta wa Yaakub kura-kuransa tare da shigar da shi Aljannatul Firdausi.

Wata sanarwa daga iyalan Yaakub ta ce:

“Lallai Allah ne Yake bayarwa, kuma Allah ne Yake karba, kuma hukuncinsa shi ne mafi alheri. Muna rokon Allah (SWT) ya gafarta masa kura-kuransa, ya shigar da shi Aljannatul Firdausi, ya kuma bai wa iyalinsa, dalibansa da daukacin al’umma karfin gwiwa da hakurin jure wannan babban rashi.”

Wani limamin Yarbawa ya rasu a Enugu

Kun ji cewa Alhaji Abdul Mutalib Badamosi, limamin Masallacin Yarbawa da ke Ibagwa-Aka, Jihar Enugu, ya riga mu gidan gaskiya.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Igbo-Eze South, Ugo Ferdinand Ukwueze kuma mataimakin shugaban ALGON na Jihar Enugu, ya ziyarci iyalan Badamosi tare da isar da saƙon ta’aziyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262