Matar Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna, ta haifa tagwaye maza

Matar Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna, ta haifa tagwaye maza

  • Daya daga cikin 'ya'yan gwamnan jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya samu karuwar yara maza tagwaye kyawawa
  • Bashir ya sanar da hakan a wallafar da yayi a Twitter inda ya ce yaran biyun maza masu kama da juna ne
  • A cewar Bashir, mahaifiyar yaran ta na lafiya yayin da ya ke cikin farin ciki, ya kara da mika godiyar sa ga Allah

Kaduna - Bashir El-Rufai, dan gwamnan jihar Kaduna tare da matar sa Halima Nwakego, sun samu karuwar yara maza biyu tagwaye.

Bashir ya na daya daga cikin 'ya'ya mazan gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Ya wallafa labarin mai dadi a shafin sa na Twitter.

Kamar yadda wallafar ta ce:

"Godiya ta tabbata ga Allah. Matata ta haifa kyawawan tagwaye maza biyu masu kama daya. Mahaifiyar ta na cikin koshin lafiya, mahaifin ya na cike da farin ciki. Na gode wa Allah. Dukkan ikon na ka ne," ya rubuta.

Kara karanta wannan

Farfesan farko na Physics, Muhammad Sani Abubakar, ya riga mu gidan gaskiya

Matar Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna, ta haifa tagwaye maza
Matar Bashir El-Rufai, ɗan gwamnan Kaduna, ta haifa tagwaye maza. Hoto daga @Bashirelrufai
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

A wani labari na daban, Bashir El Rufai, daya daga cikin 'ya'yan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fitar da hotunan kafin aurensa inda ya nuna wa duniya matar da zai aura.

Bello El-Rufai ya wallafa hotunan kashi biyu a shafinsa na Twitter inda ya yi wa hotunan lakabi da 'My Nwakaego and I'.

Matar da zai aura, Halima Nwakaego Kazaure ita ma ta wallafa hotunansu tare da rubutu na shauki da bada takaitaccen tarihin haduwarsu.

Ta nuna cewa shekaru uku da suka gabata suka fara yi wa juna sako ta kafar dandalin sada zumunta amma yanzu kuma gashi har ana shirin aure.

Asali: Legit.ng

Online view pixel