Kwanaki Kadan bayan Nasarar Pantami, Wani Babban Kusa a PDP Ya Riga Mu Gidan Gaskiya
- Jam’iyyar PDP a Gombe ta rasa mata Mataimakiyar Sakataren Kudi, Abdu Tefu Bambure, tsohon kansila mai wakiltar Dadiya Hills Ward
- Sanata Bulus Kilawangs Amos ya bayyana rasuwar Bambure a matsayin babban rashi ga al’ummar Gombe ta Kudu da kuma masarautar Dadiya
- An ce Bambure ya rasu ne ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe bayan doguwar jinya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Gombe, Nigeria - Jam’iyyar PDP a Jihar Gombe ta yi rashin Mataimakin Sakataren Kudinta, Abdu Tefu Bambure, wanda ya taba rike kujerar kansila mai wakiltar mazabar Dadiya Hills.
An bayyana Bambure a matsayin jajirtaccen mai tattara jama’a, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban siyasar al’umma a yankin karamar hukumar Gombe ta Kudu kafin rasuwarsa.

Source: Facebook
Sanata Bulus Kilawangs Amos, wanda ya wakilci Gombe ta Kudu a Majalisar Dattawa, ya tabbatar da rasuwar jigon PDP a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027
Legit.ng ta gano cewa Tefu Bambure ya rasu ne ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe, bayan fama da doguwar rashin lafiya.
Sanata Amos ya yi jimami
A cikin sanarwar da ya fitar ranar Juma’a, 2 ga Oktoba, tsohon dan majalisar tarayya ya mika ta’aziyyarsa ga Masarautar Dadiya da iyalan marigayin.
A cewar Sanata Amos, rasuwar Bambure babban rashi ne ga al’ummarsa da ma daukacin yankin mazabar majalisar dattawa ta Gombe ta Kudu.
Ya ce marigayin jami’in PDP ne da ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunkasa harkokin siyasar al’umma a yankin a tsawon rayuwarsa.
Sanarwar ta ce:
“Sanata BK ya karbi labarin rasuwar marigayin cikin kaduwa, yana mai bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ba kawai ga mutanen Dadiya ba, har ma ga daukacin mutanen yankin Gombe ta Kudu.
"Marigayin, har zuwa rasuwarsa, ya kasance mai tattara jama’a wanda ya bayar da gagarumar gudummawa ga ci gaban siyasar yankin, bayan ya taba zama kansila mai wakiltar Dadiya Hills.”

Kara karanta wannan
Babbar magana: An yi yunkurin kashe ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a Najeriya
Amos ya yi addu’ar Allah Ya ji kan Bambure, sannan ya bukaci iyalan marigayin da su dogara ga imaninsu a yayin wannan lokaci na bakin ciki.

Source: Original
Al’ummar Dadiya sun shiga jimami
Haka kuma, al’ummar Dadiya sun yi jimamin rasuwar Bambure. Wata sanarwa daga shugabannin al’ummar ta ce:
“Al’ummar Dadiya ta yi rashin ginshiki, murya mai cike da hikima da kuma mai hada kan jama’a, wanda gudummawarsa wajen ci gaba da hadin kanmu ba za a taba mantawa da ita ba.
“Muna mika sakon ta’aziyyarmu ga iyalansa, Majalisar Gargajiyar Dadiya da dukkan masu fatan alheri.
Tsohon shugaban PDP ya kwanta dama
Kun ji cewa tsohon shugaban Jam’iyyar PDP na ƙasa, Alhaji Bamanga Tukur, ya rasu yana da shekara 91 bayan fama da rashin lafiya.
Rasuwar Tukur ta kawo ƙarshen rayuwar wani fitaccen ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa wanda ya shafe shekaru yana taka muhimmiyar rawa a harkokin gwamnati da siyasar Najeriya.
Asali: Legit.ng