Iska Mai Karfi Ta Haddasa Hatsarin Jirgi, Mata da Dama Sun Rasa Rayukansu a Najeriya

Iska Mai Karfi Ta Haddasa Hatsarin Jirgi, Mata da Dama Sun Rasa Rayukansu a Najeriya

  • Matafiya mata huɗu sun mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutane takwas ya kife a Dutse, babban birnin jihar Jigawa
  • Rahotanni sun nuna cewa an samu nasarar ceto sauran mutane huɗu a raye bayan hatsarin da ya faru a Dudduru Pond
  • Hukumar NSCDC ta yi kira ga masu amfani da hanyoyin ruwa su yi taka-tsantsan a lokacin iska mai ƙarfi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jigawa, Nigeria - Matafiya mata huɗu sun mutu bayan wani jirgin ruwa da ke ɗauke da mutane takwas ya kife a Dudduru Pond da ke Ƙaramar Hukumar Dutse ta Jihar Jigawa.

Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 4.00 na yammacin Laraba, 23 ga Satumba, 2026, a tafkin da ke kusan kilomita uku daga ƙauyen Kwadige.

Jirgin ruwa.
Wasu jiragen kwale-kwale suna tafiya a kan ruwa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Daily Trust ta ruwaito cewa Hukumar Tsaro da Kare Fararen Hula ta Najeriya (NSCDC), reshen Jihar Jigawa, ta tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya fitar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: EFCC ya ayyana sake neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo, ta fadi dalili

Jirgin ruwa ya nutse a Jigawa

A cewar sanarwar, jirgin ruwan na ɗauke da mutane takwas daga ƙauyen Kwadige zuwa Kasuwar Chai Chai Sabuwa lokacin da ya kife yayin da yake tsallaka tafkin.

Bayanai sun nuna cewa iska mai ƙarfi da ake yi a lokacin da lamarin ya auku na cikin abubuwan da suka haddasa hatsarin, kamar yadda Premium Times ta kawo.

Mutane huɗu sun rasa rayukansu, yayin da aka samu nasarar ceto sauran huɗun a raye.

Mata 4 sun mutu a hatsarin jirgi

Waɗanda suka mutu su ne Hasiya Mu’azu, mai shekaru 13; Hauwa Lawan, mai shekaru 13; Fatima Lawan, mai shekaru 12; da Dawsiyya Lawan, mai shekaru 13.

Hukumar NSCDC ta ce an binne gawarwakin mutanen huɗun bisa tsarin addinin Musulunci. An ce manoma da ke aiki a kusa da tafkin ne suka ceto mutanen huɗun da suka tsira lokacin da hatsarin ya faru.

Kara karanta wannan

An ga tashin hankali da 'yan bindiga suka kashe mataimakin kwamandan rundunar tsaro a Plateau

Mazauna ƙauyukan Kwadige da Kuna su ma sun shiga aikin ceto da kwashe waɗanda abin ya shafa.

Hukumar NSCDC ta yi ta’aziyya

Kwamandan NSCDC na Jihar, CC Muhammad Kabiru Ingawa, ya jajanta wa iyalan waɗanda suka mutu da kuma al’ummar Kwadige baki ɗaya kan wannan babban rashi.

Ya buƙaci mazauna da ke amfani da hanyoyin ruwa wajen sufuri su yi taka-tsantsan sosai, musamman a lokacin da ake samun iska mai ƙarfi da kuma mummunan yanayi.

Jigawa.
Taswirar jihar Jigawa da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Kwamandan ya kuma shawarci masu tukin jiragen ruwa da fasinjoji su kiyaye matakan tsaron ruwa, tare da guje wa yin tafiya a lokacin da yanayi zai iya jefa rayuka cikin haɗari.

NSCDC ta yi kira ga al’ummomi da masu amfani da jiragen ruwa su bai wa tsaro fifiko domin kauce wa sake faruwar irin wannan mummunan lamari a hanyoyin ruwa na jihar.

Jirgin ruwa ya yi ajalin mata 3 a Kano

A wani labarin, kun ji cewa ’yan mata uku daga gida ɗaya sun mutu bayan kwale-kwalen da suke ciki ya kife a tafkin Tiga Dam da ke jihar Kano.

'Yan matan da suka riga mu gidan gaskiyar ’yan asalin ƙauyen Yalwan Rugu-Rugu ne, da ke ƙaramar hukumar Tudun Wada ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262