'Dan Jagoran APC, Bashir El-Rufai zai auri 'Diyar kusa a PDP, Halima Kazaure
- Bashir Nasir El-Rufai ne zai auri ‘Diyar Ibrahim Kazaure, Halima
- Sanata Ibrahim Kazaure ya na cikin kusoshin PDP a yankin Arewa
- Kazaure ya rike mukamai da-dama a baya a Gwamnatin Najeriya
Abin da jama’a su ke tambaya shi ne, wanene Ibrahim Kazaure OFR, Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Arewa maso yamma a yau?
Ibrahim Kazaure ya taba rike kujerun Minista, Ambasada da kuma Sanata a lokacin da soji da jam’iyyar PDP ke rike da gwamnatin tarayya a kasar.
Kazaure OFR mai shekaru 66 ya dade ya na harkar siyasa, ya na cikin wadanda Sabo Bakin-Zuwa ya nada a matsayin kwamishinoninsa a 1983 a Kano.
KU KARANTA: Hoton katin gayyatar daurin auren El-Rufai da Kazaure
Ban da siyasa a tsohuwar jihar Kano, shugabanni sun yi da Kazaure a gwamnatin tarayya.
Bayan sojoji sun kifar da gwamnatin farar hula a 1983, Kazaure ya koma siyasa a lokacin da Janar Ibrahim Babangida ya sake buga tambura a 1992.
A wancan lokaci ne Ibrahim Kazaure ya zama daya daga cikin Sanatocin farko da su ka wakilci jihar Jigawa, wanda a lokacin ta balle daga Kano.
Tsakanin 2003 da 2007, Kazaure ya zama Jakadan Najeriya zuwa kasar Saudi Arabia. Da Ummaru ‘Yar’adua ya hau mulki, sai ya nada shi Minista.
KU KARANTA: Bashir El-Rufai ya caccaki masu sukar hotunan bikinsa
Sanata Kazaure ya rike kujerar Ministan ayyuka na musamman da kwadago da aikin yi har zuwa lokacin da Goodluck Jonathan ya yi zazzaga a 2010.
Labarin da ke yawo a halin yanzu a shafuka da dandalin sada zumunta shi ne Bashir Nasir El-Rufai ne zai auri Halimah Ibrahim Kazaure esq.
Amarya Halima Kazaure kuwa ta yi karatu ne a jami’ar Reading da ke kasar Ingila, ta karanci ilmin shari’a tsakanin 2015 zuwa shekarar 2018.
Mahaifiyar Halima Kazaure Ibo ce daga kudancin Najeriya, mahaifinta kuma mutumin Jigawa.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng