Ministan Tinubu Ya Koya wa Atiku da Obi Karatu game da Tallafin Man Fetur

Ministan Tinubu Ya Koya wa Atiku da Obi Karatu game da Tallafin Man Fetur

  • Heineken Lokpobiri ya ce a yanzu Najeriya ba ta da kudin da za ta kashe kan tallafin man fetur
  • Karamin ministan harkokin man ya ce ta kai ana kashe N18bn a kullum saboda fetur ya yi sauki
  • Da yake sukar ‘yan adawa, Lokpobiri ya nuna babu inda gwamnati za ta samo kudin da za a biya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Bayelsa - Heineken Lokpobiri, wanda shi ne karamin ministan arzikin mai a Najeriya ya soki masu alkawarin dawo da tallafi.

Ministan harkokin man ya bayyana cewa maido tsarin tallafin fetur ba a abu ne mai bullewa a halin da ake ciki a kasar a yau ba.

Atiku Abubakar
Atiku Abubakar, Peter Obi, Kashim Shettima, Rabiu Kwankwaso da wasu manya a taro a Abuja Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan mai ya yi kaca-kaca da tsarin tallafi

The Cable ta ce Heineken Lokpobiri ya yi wannan bayani ne lokacin da ya yi wata zantawa da manema labarai a garin Yenagoa.

Kara karanta wannan

Amaechi ya fayyace saukin da za a samu tun shekarar farko idan Atiku ya kafa gwamnati

Hakan ya zama raddi musamman ga Atiku Abubakar wanda ya ce muddin aka zabe shi, sai an kuma dawo wa da tallafin man fetur.

Shi ma Peter Obi ya dawo kan matsayar, ya ce zai dawo da shi idan an cire barnar da ake yi.

Lokpobiri ya yi tir da maganganun manyan ‘yan adawa, yana mai mamakin inda za a ga kudin da za a biya domin mai ya sauka.

“Daga ina kudin zai fito?”
“Ana sa ran kudin ya fito ne daga harkokin mai”

Illar da tsarin tallafin mai ya yi

Sanata Lokpobiri ya yi wa ‘yan jarida bayani cewa tsarin ya taimaka wajen kwashe arzikin Najeriya, abin da yanzu ba za a iya ba.

Ministan ya ce ba don matakin da aka dauka na barin farashin fetur hannun ‘yan kasuwa ba, da Najeriya ta zama kamar Venezuala.

Ya ce a halin yanzu, mutanen kasar Venezuala sun samu kan su a wani irin bakin talauci da ko burodi mutum ba zai iya saye ba.

Kara karanta wannan

'Da Bello Turji ne da tuni sun sake shi': Malami kan tsare Nnamdi Kanu a Sokoto

Sannan ya ce lokacin da Bola Tinubu ya hau mulki, an yi lassafin cewa ana kashe N18.4bn kullum saboda man fetur ya yi araha.

This Day ta rahoto shi yana cewa sai Najeriya ta rika kashe N21tr a kowace shekara da a ce Tinubu bai daina biyan tallafin fetur ba.

Cire tallafin mai ya gyara aikin NNPCL

Baya ga haka, ya ce kamfanin NNPC ya zama bai iya ba gwamnatin tarayya wani kudi a lokacin da ake fama da tallafi.

Heineken Lokpobiri ya ce:

“Idan za ku tuna NNPC bai taba biyan wani kudi ba. Kamfanin NNPC bai taba cin wata riba ba gaba daya.
"Abin da suke yi shi ne fita da danyen mai, sai su shigo da kayan da aka tace. NNPP kadai yake kawo mai.”

Minista ya fadi matsalar hako danyen mai

Ban da matsalar NNPC, ministan ya ce Najeriya tana da ikon hako ganguna miliyan 2.5 zuwa miliyan uku na danyen mai.

Amma ya ce abin da ake iya hako wa a rana bai kai haka ba saboda rashin kayan aiki.

Kara karanta wannan

‘Yan Keke Napep sun rungumi tafiyar TinubuMustGo domin hana APC zarcewa a 2027

A karshe ya ce ana kokarin samar da sababbin bututu domin NNPC ya iya aika mai, sai dai ya nuna cewa aikin zai dauki lokaci.

Gidan mai
Wani gidan man kamfanin Oando a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: UGC

ADC ta dage katun maido tallafi

Ana da labari cewa za a ɗauki matakan rage tsadar sufuri, farashin man fetur da na kayan abinci a kasuwa idan aka canza gwamnati.

Rotimi Amaechi ya ce za a yi wannan idan jam’iyyar adawa ta samu nasara a zaɓen 2027 a kan Bola Ahmed Tinubu da jam'iyyarsa ta APC.

Ya ce manufofin gwamnatin da za su kafa ita ce mayar da hankali a farfaɗo da tattalin arziki da kuma ganin talaka ya samu saukin rayuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng