
Hotunan Aure







An daura auren 'ya'yan Sanata Rabi'u Kwankwaso, Sanata Barau jibrin, Danjuma Goje, Gwamna Umar Namadi da Gwamnan Delta da sauran 'yan siyasa a 2024.

Bidiyon auren G-Fresh Alameen da Alpha Charles ya haddasa ce-ce-ku-ce a TikTok, inda wasu ke yaba auren, wasu kuma na nuna damuwa game da bambancin addini.

An daura auren Dr Salma Umar A. Namadi a jihar Jigawa. Gwamnoni da manyan 'yan Najeriya ne suka hallara daurin auren a babban masallacin Dutse na Jigawa.

Sanata Barau Jibrin ya yi godiya ga manyan mutane da suka halarci daurin auren 'ya'yansa da na sarkin Bichi, Nasiru Ado Bayero a masallacin kasa na Abuja.

‘Dan Ministan kasafin kudin Najeriya ya auri sahibarsa, Amina Tatari Ali a Kaduna. An daura auren Ibrahim A. Bagudu da Amina ne a masallacin nan na Sultan Bello.

Fitaccen mawakin Kannywood, Auta Waziri ya na gayyata daukacin masoyansa zuwa daurin aurensa a ranar Juma'a, 6 ga watan Disambar 2024. Ya saki zafafan hotuna.

Ma'aurata mafi tsufa a duniya sun syi aure yayin da suka haura shekaru 100. Angon dan shekaru 100 ya auri yar shekaru 102. Yan uwa sun shaida auren.

Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya sauka a Kano domin halartar daurin auren yar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da aka gudanar a yau Asabar.

Tsohon gwamnan Gombe, Sanata Danjuma Goje ya musanta cewa an rika watsa kudi a bkin ‘yar sa, Fauziyya Danjuma Goje da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja.
Hotunan Aure
Samu kari