FEC: Gwamnatin Tinubu Ta Amince a Kashe N438bn wajen Yin Tituna a Najeriya

FEC: Gwamnatin Tinubu Ta Amince a Kashe N438bn wajen Yin Tituna a Najeriya

  • Bello Goronyo ya ce an amince da ayyukan gyara da sake gina muhimman hanyoyi a jihohin Ekiti, Rivers da Ogun
  • Za a gina sabon filin ajiye manyan motoci a Aro-Ngwa da ke jihar Abia don rage cunkoso a kan manyan hanyoyi
  • Ministan ayyukan ya ce gwamnatin ta mika wasu hanyoyi ga kamfanoni masu zaman kansu karkashin yarjejeniyar PPP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Majalisar zartarwa ta tarayya wato FEC ta amince da aikin gini da gyaran hanyoyi da za su ci N438bn a kasar nan.

Matakin da aka dauka ya hada da amincewa da aikin tashoshin tireloli da wasu manyan hanyoyi a wani tsari da ‘yan kasuwa.

Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a bakin aiki a Aso Rock Hoto: Olusegun Dada
Source: Facebook

Minista ya yi magana bayan taron FEC

Karamin ministan ayyuka na Najeriya, Bello Goronyo, ya bayyana haka da yake zantawa da ‘yan jarida a cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Tinubu ya dauki sabon mataki kan tsaro, ya ba da wa'adin kwanaki 90

Ministan ya fadi makomar zaman da aka yi a fadar shugaban kasa a ranar Laraba 19 ga Agusta 2026.

Ya ce majalisar FEC ta duba takardu kusan 15 da ma’aikatu dabam-dabam suka gabatar, daga ciki har da bakwai daga ma'aikatarsu.

Bello Goronyo ya ce Majalisar ministoci ta amince a gyara titin kan iyaka na Ado-Ekiti-Iyin-Aramoko-Itawure-Osun a jihar Ekiti.

Ya kuma ce kamfanin Messrs CBC Global Civil and Building Construction Nigeria Ltd. Zai yi aikin hanyar a kan kudi N159.83bn.

Gwamnatin tarayya ta amince da karin wasu ayyuka

An kuma yi na’am da wasu sauye-sauye da aka samu a aikin titin Abeokuta-Iboro-Ilaro sakamakon canjin kwalta zuwa siminti.

A Rivers, Majalisar FEC ta amince da aikin titin Port Harcourt-Eleme Junction-Onne a N74bn.

Goronyo ya shaida cewa akwai aikin titunan Ado-Ekiti zuwa jami’ar Afe Babalola a Ekiti da hanyar Ilara-Iselu da za a yi a Ogun.

Wadannan aikace-aikace suna cikin kokarin gwamnatin Bola Tinubu na amfani da bangaren sufuri domin bunkasa tattalin arziki.

Kara karanta wannan

Sojojin sama sun yi barin wuta kan yan ta'adda, miyagu da dama sun rasa rayukansu

'Yan kasuwa za su gina tashar manyan motoci

Game da tashoshin tirela, minista ya ce FEC ta amince a hada-kai da ‘yan kasuwa domin dauke manyan motoci daga kan hanya.

PM News ta rahoto cewa ‘yan kasuwa ne za su dauki alhakin tsarawa, fitar da kudi, ginawa da kuma kula da tashoshin manyan motocin.

Za a samar wa motocin greenfield tasha a Aro-Ngwa a jihar Abia. Kamfanin Greg Jane International Ltd zai yi aikin a kan N19.70bn.

A karshe karamin ministan ya gode wa shugaban kasa saboda ayyukan da za a yi a fadin Najeriya.

Titi.
Wani titi dauke da motoci a Najeriya Hoto: Getty Images
Source: Instagram

Minista: Gwamnati za ta rusa gidajen manya a Abuja

Nyesom Wike ya umarci a rushe dukkan gidajen da aka gina a kan hanyoyin ruwa a Abuja kamar yadda aka rahoto a makon nan.

Hakan ya zama dole ne a sakamakon ambaliya da aka samu a wasu unguwanni a Abuja, abin da ba a saba gani a babban birnin ba.

Ministan Abuja ya ce za su rushe duka gidajen da aka samu kan hanyar ruwa duk da wasu gidajen na sanatoci da manyan mutane ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng