Doguwa Ya Fito da Abubuwa 2 da Za Su Ceci APC daga Shan Kaye a Jihar Kano a Zaben 2027
- Dan majalisar Doguwa/Tudun Wada, Alhassan Ado Doguwa, ya ce sabon sauyin siyasa da hadin kan APC zai karfafa damar jam’iyyar a Kano a zaben 2027
- Doguwa ya bukaci mambobin APC da magoya bayanta su hada kai domin samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakai
- Ya amince da cewa cire tallafin fetur da sauye-sauyen haraji na jefa ’yan Najeriya cikin wahala, yana mai cewa ana iya sake duba manufofin idan ya zama dole
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Doguwa/Tudun Wada ta tarayya, Hon. Alhassan Ado Doguwa, ya bayyana abubuwan da za su taimaki APC a jihar Kano.
Doguwa ya ce sabon sauyin siyasa da kuma karuwar hadin kai a cikin APC za su sanya jam’iyyar cikin kyakkyawan matsayi na samun nasara a Jihar Kano a babban zaben 2027.

Kara karanta wannan
Ba ɓoye ɓoye, Gwamna Sule ya faɗi jihohi 3 da APC ke fuskantar babban ƙalubale gabanin 2027

Source: Facebook
Doguwa ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi ga al’ummar mazabarsa a Karamar Hukumar Doguwa ta Jihar Kano,nkamar yadda Leadership ta ruwaito.
Abubuwan da za su taimaki APC a Kano
Ya bukaci mambobin APC da magoya bayanta su yi aiki tare a matsayin iyali domin tabbatar da nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.
Ya ce haduwar bangarorin siyasa da a baya suke adawa da juna ta samar da wani sabon dandali na hadin kai da hadin gwiwa a Doguwa da Tudun Wada.
A cewarsa, wannan ci gaba ya hada tsoffin abokan hamayyar siyasa karkashin inuwa guda, tare da samar da damar da za ta bai wa dukkan mambobin jam’iyyar damar yin aiki tare domin ci gabanta.
Ya ambaci Shugaban Karamar Hukumar Doguwa, Alhaji Umaru Haruna, da sauran masu ruwa da tsaki a matsayin wasu daga cikin wadanda yanzu suke aiki a karkashin APC.
Ya ce sabon ci gaban ya sauya yanayin siyasa a yankin, inda tsofaffin abokan hamayya yanzu suke aiki domin nasarar APC da gwamnatin Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Babban malamin addinin musulunci a Najeriya, Sheikh Yaakub ya rasu
Doguwa ya yi kira ga hadin kai
Doguwa ya ce:
“Yanzu mun kai matsayin da ya kamata, kuma mun samu damar yin aiki cikin daidaito saboda dukkanmu, duka bangarorin da suke adawa a baya da kuma manyan kungiyoyin da suke cikinmu yanzu da kuma wadanda suke a baya, duk sun hade karkashin inuwa guda kuma suna da matsaya guda.”
“Muna aiki a matsayin iyali. Muna aiki a matsayin gungun mutane da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, kuma za mu ci gaba da tabbatar da cewa APC ta samu nasara daga sama har kasa.”
Doguwa ya tabo manufofin Tinubu
Dangane da manufofin tattalin arziki na gwamnatin tarayya, ciki har da cire tallafin man fetur da sauye-sauyen haraji, Doguwa ya amince da wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta.
Dan Majalisar ya ce ana iya sake duba manufofin gwamnati da dokokinta idan ya zama dole.

Source: Twitter
Doguwa ya ce a matsayinsa na wakilin jama’a, zai ci gaba da isar da damuwar al’umma ga Shugaba Tinubu da sauran masu tsara manufofi.

Kara karanta wannan
Dan Takarar Shugaban Ƙasa Ya Faɗi dalilin da Ya Sa Tinubu ke Son Komawa Ƙarfi da Yaji
Doguwa ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, kan ayyukan da ya ce gwamnatinsa ta cimma a fannonin samar da ababen more rayuwa da bunkasa rayuwar jama’a.
Yarbawan Kano za su tarawa Tinubu kuri'u
Kun ji cewa ɗan Majalisar Wakilai, Leke Abejide, ya ƙaddamar da shirin wayar da kan al’umma da tallafa wa Yarbawa miliyan 1 da ke Kano domin goyon bayan Bola Tinubu.
Abejide, wanda ke wakiltar mazaɓar Yagba ta Tarayya a jihar Kogi, ya kafa kwamiti mai mutum 27 da zai jagoranci shirin a ƙananan hukumomin Kano 44
Asali: Legit.ng