Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka

- Bello El-Rufai ya sake fitar da sabbin hotunansa tare da matar da ya ke shirin aure Halima Nwakaego

- Sabbin hotunan kamar na farko suma sun janyo cece-kuce da mahawara a dandalin sada zumunta musamman Twitter

- Mutane da dama sun nuna takaicinsu kan irin shiga da runguma da Bello ya yi a hoton wasu kuma suna ganin ba komai bane

Dan gwamnan Jihar Kaduna, Bello El-Rufai ya sake fitar da wasu sabbin hotunansa tare da matar da zai aura mai suna Halima Nwakaego Kazaure.

Bello ya wallafa hotunan ne a shafinsa na Twitter a ranar Talata 17 ga watan Nuwamban 2020.

Hotunan sun nuna Bello tare da Nwakaego a wani wuri mai kyau tare da furanni a bayansu sun kuma riko juna.

DUBA WANNAN: 'Yan jam'iyyar APP 20,000 ciki da shugbansu sun koma PDP a Ebonyi

Irin wannan yanayin da suka dauki hotunan ya janyo cece-kuce musamman a shafin Twitter inda wasu da dama suka janyo hankalin Bello cewa abinda ya yi ya saba wa koyarwar addinin musulunci har ma da al'addar bahaushe dan arewa.

Ko a kwanakin baya ma Bello El-Rufai ya fitar da wasu hotunan biyu tare da suka dauka tare da sahibarsa Halima Nwakaego.

Wasu mutanen kuma suna ganin bai dace a tsaya ana bata lokaci a kan hotunan da ya wallafa a a yayin da matsaloli irin na tsaro da sauransu na addabar mutane.

KU KARANTA: Buhari na buƙatar goyon baya don magance sheɗanun da ke Najeriya, in ji Tambuwal

Ga dai wasu daga cikin ra'ayoyin mutane da suka yi tsokaci a shafin na Twitter.

@AbdulMalumfashi1 ya ce, "Kaji tsoron Allah Bashir. Wannan hoton bai dace dakaiba.

@oluwatosinodun2 ya ce, "Ina takaicin yadda aka hada ni kasa daya tare da irinku. A maimakon ku mayar da hankali kan yi wa shugabanni magana game da rashin tsaro kun fiye damuwa da abinda wani ke yi a rayuwarsa. Duk abinda mutum ya ga daman bautawa matsalarsa ne.

@Kaneem7 ya ce, "A lokacin da @Rahma_sadau ta wallafa hotuna, kun yi ta mata fada amma yanzu babu wanda ke magana... Ina muku fatan alheri.

@BABANZAURE22 ya ce, "Fada alheri ko kayi shiru. Me yasa zaka yanke hukunci bayan Allah ne Alkalin Alkalai.

@soltan212 ya ce, "Saba dokokin Allah da Manzonsa ba zai haifar maka alheri a aurenka ba. Kana bukatar albaraka Allah a gidanka fiye da yabon da mutane za suyi maka. Ya Allah ka yi magana jagoranci @hadizel

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka
Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka. Hoto daga @BashirElRufai
Asali: Twitter

Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka
Hotunan Bashir El-Rufai rike da ƙugun Halima Nwakaego sun janyo masa caccaka. @BashirElRufai
Asali: Twitter

A wani labarin da Legit.ng ta wallafa, gwamnatin Jihar Kogi za ta bullo da sabon haraji a kan kowanne gasashen burodi a jihar kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ma'aikatar kasuwanci da masana'antun tace harajin zai taimaka wajen kara samun kudaden shigar da ake samu na cikin gida.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164