Babbar Magana: Ƴan Bindiga Sun ba Iyayen Yan NYSC da Aka Sace Wa'adin Awa 24

Babbar Magana: Ƴan Bindiga Sun ba Iyayen Yan NYSC da Aka Sace Wa'adin Awa 24

  • Iyalan matasan NYSC 20 da aka sace a kan hanyar zuwa sansanonin horo sun ce masu garkuwa sun ba su wa’adin sa’o’i 24
  • Masu garkuwa sun bukaci a biya Naira biliyan ɗaya, wato Naira miliyan 50 ga kowane mutum, domin sakin matasan da aka sace
  • Kwamishinan ’yan sandan Imo ya ce an gano sansanin masu garkuwar ta amma an dakatar da samamen saboda abubuwan fashewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ibadan, Oyo - Iyayen matasan NYSC 20 da aka sace yayin tafiya daga Oyo zuwa sansanonin horo sun ce masu garkuwa sun ba su wa’adin sa’o’i 24.

Iyayen sun bayyana hakan ne ranar Asabar lokacin da suka ziyarci Olubadan na Ibadanland, Oba Rashidi Ladoja, a gidansa da ke Bodija, Ibadan.

An sace ƴan NYSC 20 a Imo
Taswirar jihar Imo da aka sace wasu matasa yan NYSC. Hoto: Legit.
Source: Original

Rahoton PUNCH ya ce matasan 20 da suka kammala karatu suna tafiya daga Ibadan zuwa sansanonin NYSC ranar Alhamis, lokacin da wasu ’yan bindiga suka kai musu hari.

Kara karanta wannan

Iyaye sun shiga ha’ula’i, ‘yan bindiga sun bukaci N950m kafin sakin masu NYSC

Kwamishinan ’yan sandan Oyo, Olugbenga Abimbola, da Aseyin na Iseyinland, Oba Sefiu Adeyeri, sun halarci ganawar da iyalan suka yi da Ladoja.

’Yan bindigan sun tare motocin bas guda biyu da ke dauke da matasan a kan titin Owerri-Onitsha, a Umunoha, Jihar Imo.

Rahotanni sun ce masu garkuwar sun bukaci a biya Naira miliyan 50 kan kowane mutum, wanda ya kai Naira biliyan ɗaya gaba ɗaya.

Manajan Daraktan Uko Akwa Ibom Motors Nigeria Limited, Isiah Akpan, ya tabbatar cewa da bukatar kudin fansar ranar Juma’a.

Da take magana a madadin iyalan, Alhaja Akande da Oyebola Akande sun ce masu garkuwar suna tuntubarsu ta wayoyin matasan da aka sace.

Sun ce masu garkuwar sun fara kiran su tun ranar Juma’a, suna neman Naira miliyan 50 kan kowane matashi tare da barazanar cutar da su.

Iyayen sun ce ba za su iya tara irin wannan makudan kudin a halin yanzu ba, don haka suka roki Ladoja ya taimaka wajen ceton ’ya’yansu.

Sun kuma roki Ladoja da kwamishinan ’yan sanda su shiga tsakani domin tabbatar da an saki ’ya’yansu cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Jami'an tsaro sun yi barazanar cafke Sarki Sanusi II da Aminu Ado Bayero a Kano

A nasa bangaren, Ladoja ya tabbatar wa iyayen cewa ana kokarin ceto matasan lafiya ba tare da an cutar da su ba.

Ya ce za a sanar da iyalan duk wani bayani da aka samu, yana mai cewa ’yan sanda suna aiki dare da rana domin ganin an ceto su.

Shi ma Kwamishinan ’yan sandan Oyo, Olugbenga Abimbola, ya ce ya tuntubi takwaransa na Imo kan lamarin tun bayan faruwar satar.

Ya ce kwamishinan ’yan sandan Imo ya tabbatar masa cewa za a ceto wadanda aka sace ba tare da an cutar da su ba.

Kwamishinan bai bayyana ko an biya wani bangare na kudin fansar ba, sannan bai yi karin bayani kan ayyukan ceto da ake gudanarwa ba.

Wannan sabon ci gaban ya zo ne yayin da hukumomin tsaro ke kara kaimi wajen ganin an ceto matasan da aka sace.

Kwamishinan ’yan sandan Imo, Audu Garba Bosso, ya ce jami’an tsaro sun gano sansanin da ake zargin ana tsare da sauran wadanda aka sace.

Ya ce an gano sansanin ne ta amfani da jiragen sama marasa matuƙi, amma aka jinkirta kai samamen saboda bayanan sirri sun nuna cewa an dasa abubuwan fashewa na IED a sansanin.

Kara karanta wannan

Abin da ake tsoro ya zama gaskiya, ‘yan sanda sun tabbatar da sace ‘yan NYSC

Sufeto-Janar na ’yan sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya kuma tura Mataimakin Sufeto-Janar mai kula da ayyukan rundunar, Shehu Nadada, zuwa Imo domin jagorantar aikin ceto.

Karin bayani na tafe....

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.