Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun dauki hankulan 'yan Najeriya

- Bashir El-Rufai, dan gwamnan Kaduna ya fitar da hotunan kafin aurensa da Halima Nwakaego Kazaure

- Ganin cewa akwai sunan Ibo cikin sunan matar yasa wasu da dama sun ta tofa albarkacin bakinsu kan hotunan

- Wasu na ganin dabara ce kawai ta siyasa don samun goyon bayan mutanen kudu yayin da wasu kuma abin ya basu sha'awa sun masa fatan alheri

Bashir El Rufai, daya daga cikin 'ya'yan gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya fitar da hotunan kafin aurensa inda ya nuna wa duniya matar da zai aura.

Bello El-Rufai ya wallafa hotunan kashi biyu a shafinsa na Twitter inda ya yi wa hotunan lakabi da 'My Nwakaego and I'

Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun janyo cece-kuce
Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun janyo cece-kuce. Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun janyo cece-kuce
Hotunan shirin bikin Bashir El-Rufai da Nwakaego sun janyo cece-kuce. Hoto: @BashirElRufai
Asali: Twitter

Matar da zai aura, Halima Nwakaego Kazaure ita ma ta wallafa hotunansu tare da rubutu na shauki da bada takaitaccen tarihin haduwarsu.

Ta nuna cewa shekaru uku da suka gabata suka fara yi wa juna sako ta kafar dandalin sada zumunta amma yanzu kuma gashi har ana shirin aure.

DUBA WANNAN: Kansila ya yi wa matar yayansa mugun duka bayan zarginta da maita

Ta nuna cewa sahibinta shine kadai mutumin da ke iya jure halayenta duk da cewa wasu lokutan ta kan so sai yadda ta ke so za ayi abubuwa.

Duba da cewa matar da Bashir zai aura tana da sunar Ibo ya janyo hankulan 'yan Najeriya da dama. Wasu sun rika sukarsa don zai auri 'yar kabilar Ibo duk da kalon da wasu ke masa na ganin kamar 'yana da matsala da ibo'.

KU KARANTA: Cibiyar Lafiya ta ce ana fuskantar karancin kororon roba a wani gari a Bauchi

@Vigourjr ya ce, 'Tana da kyau. Amma ban san yadda yarinyar ke ji ba duba da ta san baka kaunar mutanen ta... idan ma dai da gaske ita ibo ce.'

@xj_clo, 'Wasu 'yan matan Ibo ba za su damu ba idan har akwai kudi.'

@ChuGalix ta ce, 'Da fatar auren ka zai yi armashi irin yadda Buhari ya mayar da Najeriya. Da fatan zai yi armashi irin yadda Buhari ya yi wa masu zanga zangar EndSARS makonnin da suka gabata.'

Wasu kuma sun ce duk dabara ce ta neman goyon bayan mutanen Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu don siyasar mahaifinsa.

@nuelchica ta ce, 'Hmmm. Akwai yiwuwar wannan wata dabara ce ta El-Rufai don samun kuri'u daga Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu. El-Rufai ya kware wurin dabara. Ina taya ka murna. Ina fatan da gaske ka keyi kuma da nufin alheri ne.'

A wani labarin daban, Bala'i ya afku a jihar Bauchi yayin da wani kwale-kwale mai dauke da mutum 23 don tsallakar dasu gona ya yi sanadiyar mutuwar mutane 18.

Kakakin rundunar yan sandan jihar Bauchi, Ahmed Wakili ne ya bayyana haka a ranar Juma'a 13 ga watan Nuwamba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164