PRP Ta Dawo da Maganar Hadaka, Ta Ce Atiku zai Yi Aiki da Obi don Kawar da Tinubu
- Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya ce babban burin haɗin gwiwar ADC, NDC da PRP shi ne ganin an kayar da Shugaba Bola Tinubu
- Baba-Ahmed ya ce batun haɗin gwiwar na nan a buɗe, ciki har da yiwuwar tattaunawa kan ɗan takarar da zai samu goyon bayan ɓangarorin da za su hade
- Ya kuma ce PRP na shirin kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta, wanda zai mayar da hankali kan batutuwan talauci, cin hanci da rashawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban jam’iyyar PRP na ƙasa, Dr Hakeem Baba-Ahmed, ya bayyana shirye-shiryen jam’iyyarsa gabanin babban zaɓen 2027.
Baba-Ahmed ya ce jam’iyyarsa na aiki tare da wasu jam’iyyun adawa ciki har da ADC da NDC domin haɗa ƙarfi gabanin zaɓen.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya bayyana haka ne a wata hira da jaridar Tribune, inda ya yi magana kan shirin PRP, haɗin gwiwar jam’iyyun adawa da kuma dabarun yaƙin neman zaɓe.
Burin hadakar 'yan adawa
Baba-Ahmed ya ce babban abin da haɗin gwiwar jam’iyyun ke son cimmawa shi ne sauya gwamnatin Shugaba Bola Tinubu a zaɓen 2027.
Ya ce duk zaɓuɓɓukan na nan a kan tebur domin tattaunawa, yayin da jam’iyyun ke duba yadda za su yi aiki tare duk da cewa kowannensu yana da ɗan takararsa.
Ya ƙara da cewa duba da tanadin doka da kuma kasancewar jam’iyyun sun riga sun tsayar da ‘yan takara, akwai wasu ƙalubale da za a fuskanta wajen cimma matsaya guda.
Sai dai ya ce tattaunawa tsakanin jam’iyyun na ci gaba, kuma shugabanninsu sun fara ziyartar juna domin ƙarfafa haɗin gwiwar.
PRP za ta fara kamfen
Da aka tambaye shi kan lokacin da PRP za ta kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓenta, Baba-Ahmed ya ce za a sanar da hakan nan ba da jimawa ba.
Ya ce jam’iyyar ba ta son gaggawar kafa kwamitin saboda kawai wasu jam’iyyu sun riga sun yi hakan, tana son samar da ƙungiyar da za ta iya isar da saƙonta ga talakawan ƙasar.

Source: Facebook
Baba-Ahmed ya ce kwamitin zai mayar da hankali kan yadda za a bayyana manufofin PRP da abubuwan da take son yi kan talauci, cin hanci da rashawa, tsaro da rarrabuwar kawuna bisa kabilanci da addini.
Ya ce za a kuma mai da hankali kan makomar matasan Najeriya da yadda za a samar musu da damar da za ta taimaka musu wajen gina rayuwarsu.
Baba-Ahmed ya ce yanayin zaɓen 2027 na iya bambanta da yadda aka saba gudanar da yaƙin neman zaɓe a baya.
INEC za ta dauki ma'aikata
A wani labarin, an ruwaito cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta buɗe shafin neman ma’aikatan wucin gadi da za su taimaka wajen gudanar da babban zaɓen 2027.
Matsayin da aka bayyana sun haɗa da jami’an kula da wuraren zaɓe, manajojin cibiyoyin rajista da jami’an tallafin fasaha, da kuma jami’an gudanar da zaɓe da mataimakansu.
An bayyana cewa shafin neman aikin zai kasance a buɗe har zuwa tsakar daren 18 ga Nuwamba 2026, inda aka buƙaci masu sha’awar neman aikin su kammala rajistarsu kafin lokacin.
Asali: Legit.ng

