Zargin Ta'addanci: Dan Majalisar Amurka Ya Ji Dadin Cafke Mahmud Adam a Najeriya

Zargin Ta'addanci: Dan Majalisar Amurka Ya Ji Dadin Cafke Mahmud Adam a Najeriya

  • Dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, ya yaba da rahoton kama Mahmoud Adam da ke jihar Plateau
  • Moore ya ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na haifar da sakamako mai kyau, tare da yabawa gwamnatin Bola Tinubu
  • An kawo rahoto cewa an kama Adam a gidansa da ke Plateau tun ranar 12 ga Satumbar 2026 da muke ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Washington DC, Amurka - Dan majalisar wakilan Amurka na jam’iyyar Republican, Riley Moore, ya yi maraba da rahoton kama Mahmoud Adam.

Riley Moore na zargin Mahmud a matsayin shugaban al'ummar Fulani a jihar Plateau da ake zargin sun kai hare-hare kan Kiristoci.

Dan majalisa Amurka ya tura sako ga Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da ɗan majalisar Amurka, Riley Moore. Hoto: @sweetbelarosyy, @RepRileyMoore.
Source: Twitter

Moore ya bayyana hakan ne a shafinsa na X ranar Asabar, 3 ga Oktoba, inda ya danganta kama Adam da hadin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya.

Kara karanta wannan

'Zan ba ku man fetur kyauta': Dan takarar gwamna a Gombe ga al'ummar jihar

Dan majalisar Amurka ya yaba gwamnatin Najeriya

Dan majalisar ya kuma yaba wa gwamnatin Najeriya kan kama Adam, yana cewa kokarin Majalisar Dokokin Amurka da gwamnatin Shugaba Donald Trump na kare Kiristoci na samar da sakamako mai kyau. Ya bukaci a ci gaba da kokarin.

Ya ce:

“Wannan babban labari ne kuma abin farin ciki ga Kiristocin Najeriya.”

A cewar rahotanni, an kama Adam da sanyin safiyar ranar 12 ga Satumba a gidansa da ke Plateau. An bayyana shi a matsayin fitaccen shugaban al’ummar Fulani mai alaka da kungiyoyin tashin hankali.

Sai dai, har yanzu hukumomin Najeriya ba su yi cikakken bayani kan yanayin kama Adam ko takamaiman zarge-zargen da ake masa ba.

Bayanai kan kama shi sun fara samun karbuwa a bainar jama’a ne a watan Oktoba.

Dan majalisar Amurka ya tsoma baki kan tsaron Najeriya
Dan majalisar wakilai daga Amurka, Riley Moore. Hoto: @RepRileyMoore.
Source: Twitter

Yadda Amurka ta damu da Najeriya

Rahoton ya ce kalaman Moore sun kara nuna yadda ake mai da hankali a Washington kan matsalar tsaron al’ummomin Kiristoci a Najeriya.

Kara karanta wannan

Yana hanyar zuwa jana'izar mahaifinsa, ƴan bindiga sun harbe matashi a Sokoto

Kasashen Amurka da Najeriya na ci gaba da hadin gwiwa wajen yaki da ta’addanci.

Gwamnatin Najeriya ba ta bayyana matsayinta kan kalaman Moore ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto. Moore ya kuma taba yin magana kan kudirin samar da ’yan sandan jihohi a Najeriya.

A ranar 11 ga Yuni, 2026, Majalisar Dattawa da ta Wakilai sun nuna kudurin gyara Kundin Tsarin Mulkin 1999 domin ba da damar rarraba ikon ’yan sanda zuwa jihohi.

Moore ya ce wannan mataki na daga cikin manufofin da ya dade yana kira da a aiwatar, musamman bayan Shugaba Donald Trump ya bukace shi da binciken zargin kisan kiyashin da ake yi wa Kiristoci a Najeriya.

Dan majalisar Amurka ya magantu kan raba Najeria

An ji cewa wani ɗan majalisar dokokin Amurka ya yi gargaɗin cewa yunƙurin ƙarfafa ra’ayin raba Najeriya zai iya ƙara tsananta matsalar tsaro a ƙasar.

Dan majalisar ya ce hakan na iya jefa Kiristoci cikin haɗari musamman a Arewa ta Tsakiya, tare da bai wa ’yan ta’adda damar ƙara ƙarfi.

Riley Moore ya kuma jaddada muhimmancin haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya wajen yaƙar ta’addanci da rikice-rikice.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.