Dangote Ya Fadada a Afrika, Ya Ci Burin Komawa Samun Ribar $35bn nan da 2030

Dangote Ya Fadada a Afrika, Ya Ci Burin Komawa Samun Ribar $35bn nan da 2030

  • Kamfanin Dangote ya fitar da manufarsa ta nan da shekarar 2030 bayan fadada kasuwancinsa a Afirka
  • Za a zuba kudi har dala biliyan takwas a sabuwar masana'antar iskar gas ta LNG da matata da za a gina a Kenya
  • Zuwa lokacin Dangote yana shirin samun abin da ya kai Dala biliyan 115 duk shekara a matsayin kudin shiga

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Rukunin Kamfanonin Dangote a Najeriya ya fito da cikakkun bayanan babban burin da yake da shi na "Vision 2030" a duniya.

Dangote yana sa ran samun kudin shiga da ya wuce dala biliyan 115 a kowace shekara a kasuwancinsa a kasashen Afrika.

Aliko Dangote
Shugaban kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote a taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Burin kamfanin Dangote nan da 2030

Jaridar This Day ta rahoto cewa a shekarar 2030, kamfanin yana fatan samun ribar da ta kai dala biliyan 35 a kowace shekara.

Kara karanta wannan

Tinubu ya roki 'yan Najeriya alfarma a 2027, ya fadi dalilin neman tazarce

Hakan yana zuwa ne bayan Dangote ya fadada kasuwancinsa a cikin kasashen nahiyar Afrika bayan karfin da ya yi a gida Najeriya.

Daga cikin wadannan harkoki da ya tsumbula, har da gina matata da kuma masana'antar sarrafa iskar gas ta LNG a kasar Kenya.

Za a kashe dala biliyan takwas wajen wannan aiki a garin Lamu da ke cikin gabashin Afrika.

Shugaban kasar Kenya ya zo matatar Dangote

Shugaban Kamfanin, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana haka lokacin da Shugaban kasar Kenya, Williams Ruto ya ziyarce shi.

Mai girma Dr. Williams Ruto da mai dakinsa Racheal sun kawo ziyara zuwa matatar man Dangote da ke Ibeju-Lekki a jihar Legas.

William Ruto, ya yaba da irin manyan ayyukan da kamfanin yake gudanarwa, musamman matatar da ke tace ganguna 650,000.

Ban da gangunan mai, wannan matata da aka bude a shekarar 2023 tana samar da tan miliyan uku na takin zamani a duk shekara.

Kara karanta wannan

Badakaloli 5 da ke wuyan Atiku Abubakar da tsohuwar matarsa ‘yar kasar Amurka

Ruto ya yaba da fasahar zamanin da ya gani a wannan matata da babu irinta a duk fadin Afrika.

Dangote zai gina wa Kenya matatar mai

A nan aka fahimci cewa shugabannin kasashe biyar cikin takwas da aka gayyata za su zo wajen kaddamar da fara aikin Lamu.

Tashar Arise ta rahoto shugaba Ruto yana cewa mutane kimanin 600, 000 za su samu abin yi daga matatun da zarar an kammala.

Da yake bayani a shafinsa na X, Shugaban Kenya ya ce aikin ya nuna irin nasarar da za a samu idan aka hada kai a nahiyar Afrika.

Dangote da hadin guiwar Gwamnatin kasar Kenya za su gina matata da masana’antar da za ta rika samar 13 MTPA na iskar LNG.

Shugaban kamfanonin Dangote
Alhaji Aliko Dangote wajen taron WEF a 2014 Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Hannun jarin matatar Dangote ya yi kasuwa

Ana da labari matatar Dangote ta samu fiye da dala miliyan bakwa (Naira biliyan 10) a cikin sa'a guda da ta buɗe sayar da hannun jari.

Sayar da hannun jarin zai ci gaba har zuwa ranar 13 ga Oktoba don tara kudi $1.6bn da za a yi amfani da su wajen kara karfin matatar.

Manufar tara kudin ita ce ninka ƙarfin matatar domin ta iya tace gangar mai miliyan 1.4 a kowace rana nan da shekaru uku masu zuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng