ACF: An Fara Wayar da kan Yan Arewa a Kano kan Sayen Hannun Jari a Matatar Dangote
- ACF ta gudanar da gangamin wayar da kan jama'a a jihar Kano kan sayen hannun jari na Matatar Dangote
- Ƙungiyar ta ce wannna aiki da tavfara na wayar da kai zai taimaka wa masu son zuba jari fahimtar yadda ake sayen hannun jarin
- ACF ta gargadi yan Najeriya da ke da niyyar zuba jari da su guji jita-jitar da ake yaɗawa a kafafen sada zumunta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ƙungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a a Jihar Kano game da sayen hannun jarin Matatar Dangote, inda ta ƙarfafa wa ’yan Arewa gwiwar shiga cikin zuba jarin.
A cewar ƙungiyar, gangamin wayar da kan da aka gudanar a Kano ranar Asabar ya kasance ne domin taimaka wa masu son zuba jari fahimtar tsarin sayen hannun jarin tare da kauce wa faɗawa hannun yan damfara.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: EFCC ya ayyana sake neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo, ta fadi dalili

Source: Getty Images
An fara yada labaran karya
Daily Trust ta ce wasu masu son zuba jari sun bayyana damuwa kan labarin da ake yaɗuwa a kafafen sada zumunta cewa matatar ba ta fara samun riba ba, kuma sayen hannun jarin na iya jefa talakawan Najeriya cikin asara.
Sai dai Shugaban ACF na Jihar Kano kuma jagoran Ƙungiyar Masu Riƙe Hannun Jari, Dr Goni Umar Farouk, ya yi watsi da waɗannan ikirari, yana mai cewa ba su da tushe.
Ya ce bayanan kuɗin matatar sun nuna cewa ta samu kuɗaɗen shiga da riba mai yawa.
ACF ta kwantar da hankulan mutane
Farouk ya ce matatar ta samar da Dala biliyan $1.82 a cikin watanni shida na farkon shekara, yayin da kuɗaɗen shigarta suka tashi daga Naira tiriliyan 9.38 a shekarar 2024 zuwa Naira tiriliyan 18.74 a shekarar 2025.
Ya kuma ce matatar ta samu ribar Naira tiriliyan 2.5 bayan cire haraji a cikin watanni shida na farkon shekarar.

Kara karanta wannan
Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira
Ya ce:
“Saboda haka, duk wanda ke cewa matatar tana yin asara, kawai yana yaɗa bayanan ƙarya ne.”
Dalilin shirya taron wyaar da kai
Farouk ya ce matakin da ACF ta ɗauka na wayar da kai an yi shi ne domin tabbatar da cewa ’yan Arewa sun samu isasshen bayani kan IPO ɗin, ta yadda za su iya yanke shawarar zuba jari
ACF ta ce za ta ci gaba da wayar da kan mazauna yankin kan tsarin sayar da hannun jarin matatar Dangite tare da ƙarfafa wa masu son zuba jari gwiwar amfani da hanyoyin da aka amince da su wajen shiga cikin shirin.

Source: Facebook
Sa’a Umar, ɗaya daga cikin mutanen da suka sayi hannun jari ta hanyar tsarin da ACF ta tanada, ta ce da farko tana da shakku kan zuba jarin, amma ta yanke shawarar shiga bayan ta samu bayanai kan yadda tsarin yake.
Wani mai zuba jari, Iliya Ado, ya ce shirin wayar da kan ya taimaka wajen magance wasu daga cikin damuwar da yake da ita a baya game da shiga cikin sayen hannun jarin.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya
Dangote ya yi wa mata tanadi
Kun ji cewa gidauniyar Dangote za ta haɗa gwiwa da gwamnatocin jihohi domin taimaka wa mata masu rauni kusan miliyan biyu su sayi hannun jari a matatar Dangote.
Dangote ya ce gidauniyar za ta kuma ba matan da suka saka hannun jari ƙarin hannun jari kyauta, domin su riƙe shi a matsayin ajiyar kuɗi na dogon lokaci.
Asali: Legit.ng