Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna, Alhaji Ibrahim Idris Ya Rasu

Lokaci Ya Yi: Tsohon Gwamna, Alhaji Ibrahim Idris Ya Rasu

  • Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu ranar Lahadi, 20 ga Satumba 2026, a Birtaniya yana da shekaru 77
  • Gwamna Ahmed Usman Ododo da tsohon Gwamna Yahaya Bello sun kai ziyara gidan marigayin da ke Abuja domin jajanta wa iyalansa
  • Ibrahim Idris ya kasance Gwamnan Kogi daga shekarar 2003 zuwa 2012, inda ya yi wa’adin mulki biyu a karkashin jam'iyyar PDP

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - An shiga jimami da tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, ya rasu ya koma ga Mahaliccinsa.

Marigayi Alhaji Ibrahim Idris ya rasu ne ranar Lahadi, 20 ga watan Satumba 2026, a kasar Birtaniya yana da shekaru 77.

Tsohon gwamnan Kogi ya rasu
Tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Ibrahim Idris Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa rasuwar marigayin a ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2026.

Bayan rasuwarsa, Gwamnan Kogi, Ahmed Usman Ododo, da tsohon Gwamnan jihar, Yahaya Bello, sun kai ziyara gidan marigayin da ke Abuja domin jajanta wa iyalansa.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Kwankwaso ya yi maganar yafewa Gwamna Abba

Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Sarauta, Abdullahi Bello, da wasu manyan jami’an gwamnatin jihar sun kasance cikin wadanda suka raka su.

Ododo da Yahaya Bello sun jajanta wa iyalan marigayin

Onogwu Muhammed, mai ba Gwamnan Kogi shawara kan hulda da jama’a, kuma Babban Sakataren Yada Labarai na tsohon Gwamna Yahaya Bello, ne ya bayyana ziyarar a wani sakon da ya wallafa a Facebook ranar Lahadi.

Ya wallafa hotunan Ahmed Usman Ododo da Yahaya Bello a gidan marigayin tare da bayyana cewa:

“Gwamnan Jihar Kogi, Mai Girma Ahmed Usman Ododo; tsohon Gwamna Yahaya Bello, CON; kwamishinan kananan hukumomi da harkokin masarautu, Hon. Abdullahi Bello; da sauran manyan jami’an gwamnati sun isa gidan marigayi tsohon Gwamna Ibrahim Idris da ke Abuja, wanda ya rasu da yammacin yau.”

Ibrahim Idris ya mulki Kogi tsawon shekaru 9

Ibrahim Idris ya zama Gwamnan Jihar Kogi a watan Mayun 2003, bayan ya lashe zaben gwamna karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP). Ya sake lashe zaben shekarar 2007, inda ya ci gaba da mulkin jihar a wa’adinsa na biyu.

Kara karanta wannan

Sanata Yari na jagorantar kamfen din Tinubu, ya yi babban rashi a rayuwa

Ibrahim Idris ya bar mulki a watan Janairun 2012, inda Idris Wada ya gaje shi a matsayin gwamnan jihar.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana musabbabin rasuwar Ibrahim Idris ba.

Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi jimamin rasuwar Idris

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wadda ke wakiltar mazabar Kogi ta Tsakiya, ta yi jimamin rasuwar tsohon gwamnan a shafinta na Facebook.

Sanatar ta bayyana Ibrahim Idris a matsayin wani muhimmin mutum a tarihin siyasar Jihar Kogi da kuma jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalan marigayin da al’ummar Jihar Kogi bisa rasuwar tsohon gwamnan.

Ododo ya je ta'aziyya
Gwamna Ahmed Usman Ododo da Yahaya Bello wajen ta'aziyyar Alhaji Ibrahim Idris Hoto: Onogwu Muhammed
Source: Facebook

Babban limami ya rasu

A wani labarin kuma, kun ji cewa Alhaji Abdul Mutalib Badamosi, limamin Masallacin Juma'a na Yarbawa da ke Ibagwa-Aka, Jihar Enugu, ya yi bankwana da duniya.

An binne Alhaji Abdul Mutalib Badamosi bisa tsarin jana’izar Musulunci. Marigayin ya kuma kasance babban dan kasuwa kuma shugaban kamfanin motoci na SMO Motors.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng