Ana Shirin Zaben 2027, An Shiga har Gida An Kashe Fitaccen Dan Siyasa a Najeriya

Ana Shirin Zaben 2027, An Shiga har Gida An Kashe Fitaccen Dan Siyasa a Najeriya

  • Rundunar ’yan sandan jihar Enugu ta tabbatar da kashe fitaccen ɗan siyasa, Prince Ikechukwu Oloto, wanda aka fi sani da “Okanga Mo”, a Nsukka
  • An gano gawar mamacin cikin jini a gidansa, yana da munanan raunuka da ake zargin an yi masa da adda a kai da cikinsa
  • ’Yan sanda sun ce sun fara farautar waɗanda suka kai harin da aikata wannan danyen aiki yayin da bincike ke ci gaba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Nsukka, Jihar Enugu – Rundunar ’yan sandan Jihar Enugu ta tabbatar da kashe fitaccen ɗan siyasa, Prince Ikechukwu Oloto, wanda aka fi sani da “Okanga Mo”, a Nsukka.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda, SP Daniel Ndukwe, ya ce an gano gawar Oloto cikin jini, yana da munanan raunuka da ake zargin an yi masa da adda a kai da cikinsa.

Kara karanta wannan

An farmaki magoya bayan Kwankwaso da Peter Obi a wurin gangamin siyasa, bidiyo ya fito

Yan sanda.
Dakarun yan sandan Najeriya a bakin aiki Hoto: PoliceNG
Source: Twitter

Jaridar Punch ta ruwaito cewa kakakin yan sandan ya bayyana haka ne yayin da yake amsa tambayoyin manema labarai ranar Juma'a, 18 ga watan Satumba, 2026.

Yadda aka gano gawar dan siyasan

Ndukwe ya ce:

“Bincike na ci gaba domin gano yanayin da ya dabaibaye kisan Ikechukwu Oloto, namiji mai kimanin shekara 53, a Nsukka.
“Rundunar ’yan sanda ta samu rahoto a ranar 17 ga Satumba, 2026, da misalin ƙarfe 5:45 na yamma cewa an same shi cikin jini a gidansa.
"Jami’an rundunar sun gaggauta zuwa wurin, inda suka same shi da munanan raunuka da ake zargin an yi masa da adda a kai da cikinsa.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa jami'ai sun yi gaggawar daukarsa zuws asibiti, amma likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa.

“An garzaya da shi asibiti, inda likitan da ke kula da shi ya tabbatar da rasuwarsa. An kai gawarsa ɗakin ajiye gawa domin adanawa da gudanar da binciken gawar, yayin da aka fara farautar wanda ko waɗanda suka kai harin," in ji shi.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

An kai masa hari a gidansa

Oloto, wanda ya fito daga Ƙaramar Hukumar Nsukka, an ruwaito cewa an kai masa hari ne a gidansa da ke Odenigbo, Nsukka, a yammacin ranar Alhamis.

Majiyoyi da dama sun ce an kashe ɗan siyasar a lokacin harin, sai dai har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan yanayin da ya kai ga mutuwarsa ba.

Taswirar jihar Enugu.
Taswirar jihar Enugu da ke Kudu maso Gabashin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Haka kuma, wasu rahotannin da ba a tabbatar da su ba sun bazu a shafukan sada zumunta cewa maharan sun yi amfani da wuƙa wajen kai harin.

Yan bindiga sun farmaki yan sanda

Kun ji cewa 'yan bindiga da ake zargin mayakan haramtacciyar kungiyar IPOB ne sun kashe yan sanda biyu tare da kona motar sintiri a garin Enugu.

Kwamishinan 'yan sanda ya bada umarnin kamo maharan da suka tsere da raunukan harbin bindiga bayan musayar wuta da jami'ai.

An ce an garzaya da jami'an asibiti domin ba su taimakon gaggawa, amma likitoci suka tabbatar da cewa rai ya yi halinsa sakamakon raunukan da suka samu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262