An ga Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Kashe Mataimakin Kwamandan Rundunar Tsaro a Plateau

An ga Tashin Hankali da 'Yan Bindiga Suka Kashe Mataimakin Kwamandan Rundunar Tsaro a Plateau

  • Mataimakin Kwamandan rundunar Operation Rainbow, CSP Dennis David Babale, ya mutu bayan samun raunukan harbin bindiga lokacin da aka farmake shi
  • Harin ya faru ne a hanyar Bokkos zuwa Barkin Ladi da ke ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya
  • Sojoji da sauran jami’an tsaro sun ƙaddamar da farmaki da farautar waɗanda suka kai harin domin kama su tare da hana sake kai hare-hare a yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - Wasu 'yan bindiga da ake zargin Fulani ne sun kashe Mataimakin Kwamandan Operation Rainbow, CSP Dennis David Babale.

'Yan bindigan sun kashe mataimakin kwamandan ne bayan sun yi wa jami’an rundunar kwanton bauna a hanyar Bokkos zuwa Barkin Ladi da ke jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Rahoton Zagazola Makama ya ce lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4:06 na yammacin Talata, 22 ga Satumba 2026, lokacin da jami’an ke tafiya a cikin motar Toyota Hilux.

Kara karanta wannan

Karya ta ƙare: Yan bindiga sun ga bala'in da ya fi ƙarfinsu, kusan 20 sun bakunci lahira

An yi wa jami’an tsaro kwanton bauna

Rahoton ya ce wasu ’yan bindiga da ba a tantance ko su wane ne ba sun buɗe wa jami’an wuta yayin da suke kan hanyarsu.

Bayan samun rahoton harin, sojojin Sector 4 na Operation Enduring Peace (OPEP) sun kai ɗaukin gaggawa zuwa wurin da lamarin ya faru.

Majiyoyi sun ce Babale ya samu raunukan harbin bindiga yayin harin kwanton baunan da 'yan bindigan suka kai.

An garzaya da shi zuwa Babban Asibitin Barkin Ladi domin samun kulawar likitoci. Sai dai daga bisani ya mutu a asibitin sakamakon raunukan da ya samu.

An fara farautar waɗanda suka kai harin

Bayan harin, sojoji tare da jami’an wasu hukumomin tsaro sun ƙaddamar da farmaki da farautar waɗanda suka kai harin a yankin.

Jami’an tsaron sun ƙara tsaurara matakan neman waɗanda ake zargin da hannu a harin tare da hana sake samun wasu hare-hare a kan hanyar.

Kara karanta wannan

Amurka ta gamu da asara da jirgin yakinta ya rikito daga sararin samaniya

Lamarin ya faru ne a lokacin da ake ƙara nuna damuwa kan matsalar tsaro a wasu sassan jihar Plateau, inda hare-haren ’yan bindiga da ramuwar gayya ke ci gaba da zama barazana ga lafiyar al’umma da jami’an tsaro.

Harin ya auku ne duk da dokar hana fita da gwamnati ta sanya a Barkin Ladi da wasu kananan hukumomi biyu na Plateau.

An kao hari a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Jami'an tsaro sun kashe 'yan bindiga

A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar haɗin gwiwar jami’an tsaro ta kashe ‘yan bindiga 18 a wani samame da aka gudanar bisa sahihan bayanan sirri a ƙaramar hukumar Bakori ta Jihar Katsina.

An sanar da samun nasarar kashe 'yan bindigan ne a cikin wata sanarwa daga Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Katsina ce ta hannun kwamishinan ma’aikatar, Dakta Nasir Mua’zu.

Ma’aikatar ta ce an gudanar da samamen ne bayan samun sahihan bayanan sirri cewa ‘yan bindigar na shirin yin garkuwa da mutane da dama domin neman kuɗin fansa a yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng