Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa Ya Ci Amanar Bola Tinubu? An Samu Bayanai

Shugaban Ma'aikatan Fadar Shugaban Kasa Ya Ci Amanar Bola Tinubu? An Samu Bayanai

  • Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya ce bai taɓa cin amanar Shugaba Bola Tinubu ba
  • Gbajabiamila ya bayyana cewa sakamakon binciken zarge-zargen da aka yi masa yanzu ya isa ga yan Najeriya
  • Tsohon shugaban majalisar wakilai ya jaddada cewa amincewarsa da ajandar Tinubu ta Renewed Hope ba ta girgiza ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Rt. Hon. Femi Gbajabiamila, ya ce bai taɓa cin amanar Shugaba Bola Tinubu ba.

Gbajabiamila ya bayyana hakan ne ranar Asabar a taron shirin tallafin da yake rabawa na 2026 da aka gudanar a filin wasa na ƙasa da ke Surulere, Legas, inda ya yi magana kan cece-ku-ce da zarge-zargen da suka dabaibaye shi a watannin baya.

Femi.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Twitter

Daily Trust ta rahoto cewa zarge-zargen sun samo asali ne daga binciken da aka gudanar kan hukumar bogi ta PFIPC, inda aka ruwaito cewa ana zargin Gbajabiamila na da hannu a kafa ta.

Kara karanta wannan

Trump ya kawo babbar matsala bayan Iran ta mika tayin buɗe Hormuz ga Amurka

Sai dai bincike daban-daban kan hukumar bogin, ciki har da wanda Majalisar Wakilai ta gudanar, sun wanke tsohon Kakakin Majalisar Wakilai daga zarge-zargen.

Gbajabiamila ya yi magana kan zarginsa

Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasar ya ce sakamakon binciken ya fito ga jama’a, yana mai cewa an bi ƙa’idar doka duk da matsin lambar da wasu ke yi na a yanke masa hukunci kafin a kammala binciken.

Ya ce:

“Watannin baya sun gwada ni ta hanyoyin da ban taɓa tsammani ba. An rubuta labarai, an yi zarge-zarge masu ban mamaki, an faɗi ƙarya, sannan aka fara tambayar amincina.
"Shekaru uku da suka gabata, mutanen Surulere da mutanen Jihar Legas, da kuma waɗanda suke sona a Najeriya, sun sanya ni cikin addu’o’insu tare da magana a madadina a lokacin da hakan ya fi muhimmanci.
“Ba zan taɓa mantawa da hakan ba. Ina godiya gare ku baki ɗaya. Yanzu komai ya bayyana, jama'a sun ga abin da masu bincike suka gano."

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ana so Tinubu ya hakura da shiga takarar zaben 2027

Ya yi alkawarin ci gaba da aiki

Gbajabiamila ya ce zai ci gaba da gudanar da nauyin da ke kansa a Fadar Shugaban Ƙasa duk da abin da ya bayyana a matsayin hare-haren da ake kai masa.

Gabaja.
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: Femi Gbajabiamila
Source: Facebook

A rahoton Punch, ya ƙara da cewa:

“Bari in yi magana a fili kuma kai tsaye ga duk waɗanda suke bayan waɗannan hare-hare. Babu adadin kuɗi, babu yawan baƙar magana ko ƙarya, ko an shirya su daga cikin gida ko daga waje, da zai sa in daina aikin da nake yi da kuma aikin da Shugaban Ƙasa ya ba ni.
“Kuma ga duk wanda ke amfani da sunana wajen ɓata wa mutane suna ko kuma ya karkatar da abin da nake nufi, ya sani cewa doka za ta kama shi.”

ICPC ta wanke Femi Gbajabiamila

Kun ji cewa ICPC ta ce ba ta gano wata hujja da ke nuna cewa Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, ya san da zaman PFIPC ba.

Hukumar ICPC ta ce babu alakar Gbajabiamila da naɗa Adeniyi Adeyemi a matsayin Darakta-Janar na hukumar bogi ta PFIPC da aka kirkira ta haramtacciyar hanya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262