An Fito da Babban Dalilin EFCC na Ayyana Neman Abdulrasheed Maina Ruwa a Jallo

An Fito da Babban Dalilin EFCC na Ayyana Neman Abdulrasheed Maina Ruwa a Jallo

  • A jiya Laraba ne hukumar EFCC ta ƙaddamar da neman tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho, Abdulrashid Maina
  • Hukumar ta bukaci hukumomin tsaro, ciki har da Hukumar Shige da Fice, su zauna cikin shirin ko-ta-kwana domin kama Maina
  • Mai magana da yawun EFCC na kasa ya fito ya yi bayani kan dalilin su na daukar wannan mataki kan tsohon jami'in gwamnatin tarayya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - A ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026 ne Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta ƙaddamar da neman tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho, Abdulrashid Maina.

Hakan na zuwa ne yayin da hukumomin tsaro a ƙasar, ciki har da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya, suka shiga shirin ko-ta-kwana, inda aka umurce su da su kama Maina a duk inda aka gan shi.

Kara karanta wannan

El Rufai ya aika sako ga 'yan uwa da abokan arziki bayan shafe fiye da kwanaki 200 a tsare

Maina.
Tsohon shugaban kwamitin gyaran tsarin fansho na Najeriya, Abdulrsheed Maina da shugaban EFCC na kasa, Olanipekun Olukoyede Hoto: @officialEFCC
Source: Twitter

EFCC ta ayyana neman Maida ruwa a jalli a wani sako da ta wallafa a shafinta na X ranar Laraba da ta wuce, inda ta wallafa hotonsa da kuma wuraren da za a kai rahoto.

An gano cewa jami’an hukumar sun kuma samu umarnin bibiyar tsohon jami’in gwamnati bayan ya gaza amsa jerin wasiƙun gayyata da aka aika masa.

Dalilin ayyana neman Maina

Kakakin hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC na kasa, Dele Oyewale, ya tabbatar da hakan a wata tattaunawar waya da wakilin jaridar Daily Trust.

“Eh, an ayyana shi a matsayin wanda ake nema fuwa a jallo. A yau (Laraba) muka ayyana shi a matsayin wanda ake nema,” in ji Oyewale a taƙaice.

Sai dai a sabuwar sanarwar da hukumar ta fitar, EFCC ta bayyana cewa Maina, ɗan asalin Biu ne a Jihar Borno, ta sake ayyana nemansa ne kan zargin karɓar kadarorin sata.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: EFCC ya ayyana sake neman Abdulrashid Maina ruwa a jallo, ta fadi dalili

Tarihin shari’ar Abdulrasheed Maina

Legit Hausa ta ruwaito cewa an gurfanar da Maina tare da ɗansa, Faisal, a ranar 25 ga Oktoba, 2019, kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi halatta kuɗaɗen haram da ɓoye kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Mai shari’a Okon Abang, wanda ya kasance alƙalin Babbar Kotun Tarayya a Abuja kafin daga bisani a ɗaga shi zuwa Kotun Ɗaukaka Ƙara, ya yanke wa Maina hukunci kan zargin satar Naira biliyan 2.

A cewar binciken masu gabatar da ƙara da kuma kotu, kuɗin na daga cikin kuɗaɗen da aka tanada domin biyan ’yan fansho hakkokinsu.

Maina.
Tsohon shugaban kwamitin gyaran fansho na Najeriya, Abdulrasheed Maina Hoto: @OfficialEFCC
Source: Twitter

An ce Maina ya yi amfani da sunayen wasu daga cikin ’yan uwansa wajen buɗe asusun bakuna ba tare da saninsu ba, inda ya ajiye kuɗi har N300m, N500m da N1.5bn a ciki.

Kotun ta ƙara da cewa Maina bai iya tabbatar da cewa kuɗaɗen da ke cikin asusun ba kuɗaɗen da aka sace ba ne. Daga bisani aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekaru 61 a gidan yari.

Kara karanta wannan

EFCC na binciken wasu malaman musulunci da limamai kan laifin kuɗi a Najeriya

EFCC ta sallami ma'aikata akalla 40

Kun ji cewa EFCC ta kori sama da ma’aikata 40 cikin shekaru biyu da rabi saboda zargin cin hanci da rashawa da almundahana.

Shugaban EFCC, Olukoyede ya ce fiye da biyar daga cikin ma’aikatan da aka kora a halin yanzu suna fuskantar shari’a kan zargin aikata laifukan da suka saɓa wa doka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: