Dangote zai Fara Samar da Wutar Lantarki a Najeriya
- Babban attajirin Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana aniyarsa ta zuba jarin fiye da dala biliyan 10 a bangaren wutar lantarki domin bunkasa masana'antu
- Dangote ya bayyana cewa sauye-sauyen manufofin gwamnati da karancin wutar lantarki na daga cikin babban kalubalen da ke dakile zuba jari a Afirka
- Ya jaddada cewa ba za a samu ci gaba ko samar da abun yi ga al'umma ba matukar ba a samar da ingantacciyar wutar lantarki da zai inganta masana'antu ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hadu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCt, Abuja – Attajirin nahiyar Afirka, Aliko Dangote, ya bayyana cewa yana shirin zuba jarin da ya wuce dala biliyan 10 a bangaren samar da wutar lantarki.
Attajirin zai dauki matakin ne domin maida hankali wajen magance matsalar lantarki a Najeriya da sauran kasashen nahiyar.

Source: Getty Images
Dangote ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na Al Jazeera, inda ya gano cewa rashin tabbatuwar manufofin gwamnati da kuma karancin wutar lantarki na jefa kasar a matsaloli.
Attajirin ya bayyana matukar damuwarsa kan yadda mutane fiye da miliyan 600 a Afirka ke rayuwa cikin duhu ba tare da wutar lantarki ba.
Matakin da Dangote zai dauka
Dangote ya jaddada cewa samar da wutar lantarki na da nasaba kai tsaye da ci gaban tattalin arziki, sannan ya ce idan har 'yan siyasa suka samar da lantarki ga jama'a, ba za su ma bukaci fitowa yakin neman zabe ba.
Ya bayyana cewa:
"Kuma ina gaya muku a cikin shekaru uku zuwa hudu masu zuwa, za a samu babban sauyi a Afirka, kuma shi yasa muke duba bangaren lantarki.
"Za mu zuba jari a harkar lantarki. Akwai harka daya ko biyu da za mu iya sokewa, kamar harkar karfe, sannan mu sa kudin a harkar lantarki. Muna son zuba fiye da dala biliyan 10 a wannan bangaren kawai."

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan mutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC
Amsa kan zargin mamaye kasuwa
Dangote ya kuma mayar da martani game da zargin da wasu ke yi masa na cewa yana mamaye kasuwa shi kadai, inda ya ce ba zai yarda wannan ya karkatar da hankalinsa daga manufafinsa ba.
Punch ta ruwaito Dangote yana kwatanta kansa da shahararren dan kwallon kafa Lionel Messi, inda ya ce dole dan wasa ya maida hankali kan kwallon maimakon kallon masu kallo a fili.

Source: Twitter
A cewarsa, gwamnati ba ta ba kamfaninsa wani gata na musamman ko ikon mallakar wani bangare shi kadai ba, illa dai tsara manufofi na bangaren da ke bude ga kowa da kowa ya zuba jari.
Shirin faɗaɗa samar da taki
A wani labarin, mun ruwaito cewa Aliko Dangote ya bayyana shirin kamfaninsa na bunkasa harkar sarrafa takin zamani na Urea daga tan miliyan 3 zuwa tan miliyan 12 domin rage dogaro da kasashen waje.
Dangote ya bayyana wannan tsari ne a yayin taron tattalin arziki na Qatar da aka gudanar a birnin New York, inda ya ce hakan zai baiwa kamfanin damar wadatar da fiye da kashi 40 na nahiyar Afirka.
Kazalika, ya tabbatar da cewa suna shirin fara sayar da hannun jarin kamfanin kafin shekarar 2028, tare da hasashen cewa zai zama kamfanin taki mafi girma a duniya baki ɗaya.
Asali: Legit.ng
