Gwamna Abba Ya Yi Alhini da Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Hukumar Alhzai Rasuwa
- Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya mika ta’aziyyarsa ga iyalan marigayi Sani Lawan Kofar Mata, wanda Allah ya yi wa rasuwa
- Hakan na zuwa ne bayan an tabbatar da rasuwar Kofar Mata, wanda ya kasance tsohon shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Kano
- Gwamnan ya ce marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen yi wa jihar Kano hidima da kula da harkokin alhazai a lokacin da yake aiki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya tabbatar da rasuwar tsohon shugaban hukumar jin dadin alhazai ta jihar, Alhaji Sani Lawan Kofar Mata.
Gwamna Abba ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalai, ‘yan uwa, abokan hulɗa da al’ummar Jihar Kano bisa rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata, wanda ya ce rasuwarsa babban rashi ne.

Kara karanta wannan
Gwamna ya ɗauki zafi da 'yan bindiga suka shiga gari, suka kashe basarake a Najeriya

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Litinin, 21 ga watan Satumba, 2026.
Abba ya yi alhinin rasuwar Kofar Mata
Abba Gida-Gida ya bayyana rasuwar Alhaji Sani Lawan Kofar Mata a matsayin babban rashi ga Jihar Kano, yana mai bayyana gudunmawar da ya bayar wajen yi wa jama’a hidima.
Ya yaba da irin hidima da dumbin gudummuwa da marigayin ya bayar tare da kula da jin daɗin al’umma, musamman a fannin harkokin alhazai na jihar Kano lokacin da yake aiki.
Gwamnan ya ce za a riƙa tunawa da marigayi Sani Lawan Kofar Mata bisa irin hidimar da ya yi wa jihar Kano da kuma gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa tsarin kula da jin daɗin alhazai.
Gwamna Abba ya yi addu'a ga marigayin
Gwamna Abba Kabir ya roƙi Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya ba shi hutu na har abada a Jannatul Firdausi.

Kara karanta wannan
Kwana ya ƙare: Tinubu ya aika saƙo da aka sanar da rasuwar tsohon gwamna a Najeriya
Haka zalika, mai girma gwamnan Kano ya kuma yi addu'ar Allah Ya bai wa iyalan marigayin, abokansa da al’ummar Kano ƙarfin jure wannan rashi da suka yi mai radadi.
Ya shawarci iyalan marigayin da su yi haƙuri, su tuna cewa mutuwa makoma ce da babu makawa kowa sai ya tafi, yana kuma addu’ar Allah Ya saka wa marigayin da alheri bisa hidimar da ya yi wa bil’adama.

Source: Facebook
"Muna rokon Allah Maɗaukakin Sarki Ya gafarta wa marigayin kura-kuransa, Ya ba shi hutu na har abada a Jannatul Firdausi, Ya kuma bai wa iyalan marigayin, abokansa da al’ummar Kano ƙarfin jure wannan rashi," in ji Gwamna Abba.
Abba ya dauki mataki kan kisan Dan Shagamu
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gillan da aka yi wa fitaccen dan soshiyal midiya Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu.
Gwamna Abba ya umarci jami’an tsaro da su gaggauta gano tare da kama dukkan wadanda suke da hannu a aikata kisan domin a gurfanar da su a gaban doka.
Asali: Legit.ng