Sojoji Sun Cafke Kwamandojin 'Yan Ta'adda da Ke da Hannu a Kisan Babban Janar a Katsina
- Sojojin Operation Fansan Yamma tare da ’yan sa-kai sun kama wasu manyan kwamandojin ƙungiyar Kachalla Maha a wani samame da aka gudanar a Katsina
- Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani babban kwamanda mai suna Samagi, wanda aka bayyana shi a matsayin muhimmin jigo a tsarin gudanar da ayyukan ƙungiyar
- Ana sa ran binciken waɗanda aka kama zai taimaka wa jami’an tsaro gano maboyar ’yan ta’addan, hanyoyin samun kayayyaki da sauran waɗanda ke da alaƙa da ƙungiyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Rundunar Operation Fansan Yamam tare da haɗin gwiwar ’yan sa-kai sun kama wasu manyan kwamandojin wata ƙungiyar ’yan ta’adda a Katsina.
Kungiyar 'yan ta'addan ana alakanta da sacewa da kashe Manjo Janar Abubakar Rabe mai ritaya a Jihar Katsina da ke yankin Arewa maso Yamma na Najeriya.

Kara karanta wannan
An farmaki magoya bayan Kwankwaso da Peter Obi a wurin gangamin siyasa, bidiyo ya fito

Source: Original
An kama manyan kwamandojin ƙungiyar
Wata majiya daga rundunar soji a Gusau, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta shaida wa jaridar Leadership cewa an gudanar da samamen ne ranar Lahadi, 20 ga watan Satumban 2026.
Majiyar ta ce jami’an tsaron sun kama wasu manyan mambobin ƙungiyar da ke aiki ƙarƙashin wani da ake kira Kachalla Maha.
Daga cikin waɗanda aka kama akwai wani babban kwamanda mai suna Samagi, wanda aka bayyana a matsayin muhimmin jigo a tsarin gudanar da ayyukan ƙungiyar.
Ana kallon kamen a matsayin babban ci gaba
Kamen manyan kwamandojin na zuwa ne a matsayin wani muhimmin ci gaba a hare-haren da jami’an tsaro ke gudanarwa domin tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuffuka da kuma raunana tsarin jagorancinsu a yankin Arewa maso Yamma.
Ana zargin waɗanda aka kama da taka muhimmiyar rawa wajen sace mutane, kashe-kashe da wasu hare-haren ta’addanci da ake dangantawa da ƙungiyar Kachalla Maha a sassan yankin.
’Yan sa-kai sun taimaka wajen gano su
Samamen ya ƙunshi dakarun sojoji na Operation Fansan Yamma da ’yan sa-kai, lamarin da ya sake nuna muhimmancin samun ingantaccen bayanan sirri daga al’umma wajen bin diddigin ’yan ta’adda da ke fakewa a wurare masu wahalar isa.
Wani fitaccen shugaban ’yan sa-kai mai suna Mamara ya ce kama Samagi da sauran manyan mambobin ƙungiyar na iya samar wa jami’an tsaro muhimman bayanan sirri.
Ya ce bayanan na iya taimakawa wajen gano shugabannin ƙungiyar, yadda suke gudanar da ayyukansu, maboyarsu, hanyoyin samun kayayyaki da kuma mutanen da ake zargin suna taimaka musu.

Source: Twitter
Sojoji sun kashe 'yan ta'adda
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojoji ta Operation Hadin Kai (OPHK) sun hallaka ’yan Boko Haram da ISWAP 1,106.
Dakarun sojojin sun kuma samu nasarar kwace fiye da N300m na kuɗaɗen haram da ke da alaka da yan ta'addan.
Manyan ayyukan sojin sun kuma kai ga cafke mutane 758 da ke taimaka wa ƙungiyoyin ’yan ta’addan wajen samar musu da kayan aiki.
Asali: Legit.ng
