'Amfanin da Soke ba da Tallafin Amurka Zai Yi ga Najeriya' - Jigon APC

'Amfanin da Soke ba da Tallafin Amurka Zai Yi ga Najeriya' - Jigon APC

  • Jigon APC mai mulki, Ayoola Lawal ya yi magana kan shirin kasar Amurka na janye tallafi zuwa Najeriya
  • Tsohon ɗan majalisar ya bayyana yadda shirin zai taimaka wa Najeriya domin inganta tattalin arzikinta
  • Lawal ya ce cewa matsalolin tsaro da rikice-rikice na bukatar mafita daga Najeriya, ba dogaro da ƙasashen waje ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigon jam'iyyar APC kuma tsohon ɗan takarar Majalisar Wakilai ya fadi muhimmancin dogaro da kai a Najeriya.

Ayoola Lawal, ya ce shirin Majalisar Wakilan Amurka na dakatar da tallafin da ƙasar ke bai wa Najeriya ya kamata ya zama darasi.

An yabawa shirin janye tallafin Amurka ga Najeriya
Shugaba Donald Trump na Amurka da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga, Donald J Trump.
Source: Facebook

Shawarar jigon APC ga Najeriya

A cikin wata sanarwa da ya fitar, Lawal ya ce maimakon damuwa da yiwuwar rasa tallafin ƙasashen waje, Najeriya ta fi dacewa ta mayar da hankali kan dogaro da kanta, cewar Punch.

Kara karanta wannan

An daure yar TikTok kan yada cewa shugaban kasa ya birne shanu 32 don cin zabe

Ya ce wannan mataki zai bai wa ƙasar damar ƙarfafa hukumominta, inganta shugabanci da kuma rage dogaro da taimakon ƙasashen waje ta hanyar amfani da albarkatunta yadda ya kamata.

Jigon APC ya ce bai kamata a ɗauki yiwuwar dakatar da tallafin Amurka a matsayin koma baya ba, domin hakan na iya zama dama ta ƙarfafa cibiyoyin ƙasa.

Kalaman nasa sun biyo bayan amincewar Majalisar Wakilan Amurka da wani gyara ga dokar kasafin kuɗi da ke neman dakatar da tallafi ga Najeriya.

Wannan gyaran ya tanadi cewa sai Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar gwamnatin Najeriya ta ɗauki matakai masu inganci wajen dakile tashin hankali da kare al'ummomi masu rauni.

An yabawa shirin Amurka na janye tallafi ga Najeriya
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Muhimmancin hadin guiwa kan rashin tsaro

A cewarsa, duk da muhimmancin haɗin gwiwa da ƙasashen duniya, zaman lafiya mai ɗorewa ba zai samu ba sai an samu ingantaccen shugabanci da hukumomin tsaro masu ƙarfi.

Lawal ya ce gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta ware manyan kuɗaɗe domin yaƙi da rashin tsaro a faɗin ƙasar, cewar Tribune.

Ya ƙara da cewa rundunar sojoji, hukumomin leƙen asiri da Rundunar Ƴan Sandan Najeriya na ci gaba da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Kara karanta wannan

Bauchi: Bala Mohammed ya yi garambawul a majalisar zartarwa, ya sauke kwamishinoni 2

Ko da yake ya amince cewa har yanzu rashin tsaro babban ƙalubale ne, Lawal ya ce ana samun ci gaba a ƙoƙarin dawo da zaman lafiya.

Ya kuma soki masu bayyana matsalar tsaron Najeriya a matsayin ta addini kaɗai, yana cewa hakan yana rage girman ainihin matsalolin da ƙasar ke fuskanta.

A cewarsa, ta'addanci, ƴan bindiga, manyan laifuka, rikicin al'umma, rikicin manoma da makiyaya da rikicin masu neman ballewa duk suna cikin tushen matsalar tsaro.

Saboda haka, ya ce ba daidai ba ne a jingina dukkan matsalolin tsaron Najeriya ga addini kawai.

Yadda Kiristoci suka aminta da Muslim/Muslim

An ji cewa wani jigo a jam'iyyar APC, Farouk Aliyu, ya ce Kiristocin Najeriya sun karɓi tikitin Muslim-Muslim yanzu fiye da yadda suka yi 2023.

Ya bayyana hakan ne bayan Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takara tare da Kashim Shettima a 2027.

A bayanin da ya yi a wata hira, Aliyu ya ce gwamnatin Tinubu ta nuna a aikace cewa ba ta nuna bambanci ko wariya ga kowane addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.